1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AFIRKA TA KUDU SHEKARU GOMA BAYAN FARKON ZABE NA DIMUKRADIYYA.

Yahaya Ahmed.March 1, 2004
https://p.dw.com/p/Bvlc

Tun shekaru 10 da suka wuce ne aka yi farkon
zaben dimukradiyya a kasar Afirka Ta Kudu, inda
bakake da fararen fata suka jeru a layi daya
suka ka da kuri'unsu. Amma har ila yau, kasar
ba ta fita daga kangin mulkin mallaka na
shekaru dari da 50 da kuma mulkin danniya da
wariyar al'uma ba. A zaben da aka yi a 1994
dai, jam'iyyar ANC, karkashin jagorancin Nelson
Mandela ce ta ci nasara. Wannan lokacin ne
kuma ke alamta wani sabon zamani a tarihin
kasar, wanda aka yi wa lakabin Rainbow-Nation a
turance. Wato kasar da ta hade duk kabilu da
al'ummomi daban-daban kamar bakan gizo. Amma a
yanzu, ban da kamfanonin yawon shakatawa da ke
neman kasuwa da wannan jigon, babu wanda ke
tunawa ma da lakabin.
Babban kalubalen da kasar ta Afirka Ta Kudu ke
huskanta dai, shi ne yadda za ta kau da duk
irin cin mutuncin da aka yi wa al'ummanta na
bakaken fata a lokacin mulkin wariya na
Apartheid. An dai kafa wani kwamiti, wanda ya
yi nazari kan azabar da jami'an tsaron
gwamnatin Apartheid din ta nuna wa al'umman
kasar, musamman ma dai bakaken fata. Amma hakan
kawai bai wadatas ba. Wata `yar jarida, bakar
fata, Zubeida Jaffer, wadda a yanzu haka take
nazari kan harkokin siyasa a birnin Cape Town,
tana daya daga cikin dimbin yawan bakaken fatar
da suka sha azaba a hannun jami'an tsaron
Apartheid. A cikin shekarun 1980, ta yi kokarin
gudanad da bincike kan wata kisa da `yan sanda
suka yi wa bakaken fata. Ta hakan ne dai aka
cafke ta, aka daure ta a kurkuku ba tare da yi
mata shari'a ba, sa'annan aka dinga yi mata
azaba iri-iri.
Tana dai cikin wadanda suka yi wa kwamitin da
aka kafa, don binciken illolin mulkin wariyar,
bayani. A nata ganin dai:-
"Da wuya mutum ya iya ba da wani bayani. Saboda
duk abin da za ka iya tunawa ne azabar da aka
yi maka shekaru da dama da suka wuce. Abin da
ya shafe ni dai, a shekraun 1980 da 1985 ne ya
auku. An gayyace ni in bayyana irin azabar da
aka yi mini. Amma ba abu ne mai sauki ba, ka
tsaya gaban dimbin yawan jama'a ka yi ta tuno
ababan da ba ka son ko mafarkinsu ne ma ka sake
yi."
Gaba daya dai, kusan mutane dubu 22 ne kwamitin
ya tabbatar cewa, an yi musu azaba a lokacin
mulkin wariyar al'umma a kasar ta Afirka Ta
kudu. Masharhanta dai na ganin cewa, yawan
mutanen da suka addaba a lokacin Apartheid din
ya fi haka. Akwai mutane da yawa a yankunan
karkara, wadanda ba a tuntube su ba, ko kuma ba
a biya su diyya ba. Sa'annan akwai kuma,
madugan mulkin Aparthied din, wadanda a halin
yanzu suke zaman sharholiyarsu, ba tare da an
yi musu wani hukunci ba, ko kuma kwamitin ya yi
musu afuwa.
Daya kalubalen da Afirka Ta Kudun ke huskanta
kuma, shi ne shawo kan yawan tashe-tashen
hankullar da ake samu a kasar, musamman ma dai
a yankunan nan na Kwazulu-Natal da Yammacin
Cape. Dalilan haka kuwa na da tushensu ne daga
halin matukar talauci da al'umman yankin ke
huskanta. Ga kuma cutar Aids da rashin
kwanciyar hankali da ke addabarsu.
Game da wadannan matsalolin dai, Sankie
Mthembi-Mahanyele, mukaddashiyar babban
sakataren jam'iyyar ANC, ta bayyana cewa:-
"Abin da ya kamata mu yi la'akari da shi, shi
ne, zaton da muke yi na cewa bayan shekaru 10
na mulkin dimukradiyya, za mu iya sake wa halin
rayuwar jama'a fasali, ba abu ne mai yiwuwa ba.
Tsarin da muka gada daga shekaru da dama na
mulkin danniya, bai tanadi koyar wa mafi yawan
al'umman kasar nan wata sana'a ba."
Wannan kuwa na daya daga cikin dalilan dasuka
janyo habakar yawan marasa aikin yi a kasar.
Bayan wargajewar mulkin Apartheid dai, duk `yan
kasar na da damar shiga ko wane aiki ko kuma
sana'a. Aamma su `yan bakaken fatar, saboda tun
da ma can, ba su sami wani kyakyawan horo ba,
sai ka ga ga aikin amma ba su da kwarewar yinsa.
Cim ma hadin kan al'umman kasar Afiirka Ta
Kudun dai, ba zai yiwu ba gaba daya, sai an cim
ma rage gibin da ake da shi yanzu tsakanin masu
abin hannunsu da matalauta. A cikin shekaru
goman da suka wuce, an gabatad da shirye-shirye
da dama, don inganta halin rayuwar jama'ar
kasar, kamarsu, gine-ginen matsugunai, da bai
wa takawa damar mallakar filaye, da kuma shirin
yaki da jahilci. Amma duk da haka, gibin da ake
da shi tsakanin talakawa da masu arziki a
Afirka Ta Kudun a halin yanzu, bai bambanta ba
da na lokacin Apartheid. Har ila yau dai,
fararen fatan ne ke rike da mukamai masu tsoka
a fannin tattalin arzikin kasar.