1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu: Ma'aikatan hakar zinari 4 sun mutu

Ramatu Garba Baba
May 4, 2018

Ma'aikatan hako zinari hudu ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan aukuwar wata girgizar kasa a yankin da ake da kamfanin hakar zinari mai suna Sibanye-Stilwater da ke a wajen birnin Johannesburg.

https://p.dw.com/p/2xBbc
Südafrika illegale Goldmine bei Soweto, Johannesburg
Hoto: picture-alliance/dpa/K. Ludbrook

James Wellsted, mai magana da yawun kamfanin ya ce akwai wasu uku da suka makale a karkashin kasa, a yayin da aka yi nasarar zakulo shida da tuni aka ruga da su asibiti don basu kulawa, girgizar kasa mai karfin maki biyu da digo biyu a ma'aunin rishta, ta auku ne a wannan Juma'a inji sanarwar kamfanin.

Tuni kungiyar ma'aikatan ma'adinai ta kasar NUM ta baiyana bacin ranta kan yawaitar hadura da ke lakume rayukan ma'aikata a kamfanin na Sibanye-Stillwater, don ko a watan Febrairu ma, kusan masu hako ma'adinai dubu daya ne suka makale a yayin aiki bayan matsalar katsewar wutar lantarki a ma'aikatar, kwanaki biyu bayan wannan wasu biyu suka mutu bayan ruftawar kasa a wata ma'aikatar hakar ma'adinai mallakar kamfanin.