1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu: An kai hari a masallaci

Abdourahamane Hassane
May 10, 2018

An kashe wani limami a cikin masallaci a Afirka ta Kudu, wanda wasu mutanen da ba a tantance ba suka yi wa yankan rago kana suka raunata wasu mutane biyu.

https://p.dw.com/p/2xVNv
Südafrika Land und Leute Kapstadt Hafen
Hoto: J. Sorges

Lamarin da ya faru a arewa maso gabashin birnin Durban a garin Verulam, masu aiko da rahotanin sun ce mutane da suka aikata kisan kafin su shiga cikin masallacin sun bayyana kansu da cewar 'yan kasar Masar ne su. Har ya zuwa yanzu dai, ba a san dalilan kai harin ba, sai dai 'yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike.