1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Afirka na kokarin wadata manoma da sabbin dabaru

March 30, 2017

Kasashe 26 na Afirka da Turai da Asiya sun baje kolin sabobbin dabarun adana kayan abinci da kyautata aikin noma. Birnin Lagos na tarayyar Najeriya ne ya dauki bakwancin taron na musayar basira don ci gaban kasashe .

https://p.dw.com/p/2aKg3
Reisanbau in Nigeria
Hoto: DW/S. Duckstein

 

A ranar Alhamis ne aka kawo karshen taron na kasa da kasa na baje kolin sabobbin dabaru da suka jibanci aikin abinci da ayyukan noma a birnin Lagos. Kasar Jamus ta halarci taron da kanfanoni sama da 40, inda shugaban tawagarta Mr Martin März ya ce " ilimin fasaha na kasar jamus da ya jibanci adana kayan abinci da sarrafashi a zamanance ne Najeriya ke bukata domin magance asarar kayan noma wanda hakan ya zama kalubale ga kasar ."

Mr K. Ravi MD da ke zaman shugaban wani kanfani da ke sarrafa abinci a kasar Indiya ya ce " Najeriya ta dauki matakin inganta fannin samar da abinci bayan da ta tabbatar da cewa farashin man fetur na ci gaba da faduwa a kasuwannin duniya. Wannan shi ya kamata ya zama abun dogaro ga 'yan kasa, kuma za mu bayar da gudunmawa don cimma manufa ."

Nigeria Tomaten auf dem Markt in Port Harcourt
Tumatir ya fara wadata a NajeriyaHoto: DW/M. Bello

Sarkin noman rani a jihar Lagos Comrade Yau Musa Sakaba ya bukaci ganin " an tashi tsaye daga jihohi da kananan hukumomin Najeriya don samun nasarar amfani da sabbin dabaru na adana kayan abinci."

To sai dai a cewar Alhaji Babagana Abubakar ya ce " Kasashen Africa sun taba gudanar da taro na fannin abinci da kayan noma, inda aka cimma matsaya na kebe kaso goma cikin dari na kasafin kudi a shekara, amma har yanzu ba a cimma komai ba."

An dade ana gudanar da irin wadannan tarurruka, amma abu daya shi ne yadda shugabanni za su sami kwarin gwiwar rungumar shirin don cimma manufa.