1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka da EU sun dauki matakan takaita gudun hijira

Mohammad Nasiru Awal/PAWNovember 12, 2015

A karshen taron kolin da suka gudanar a tsibirin Malta, bangarorin biyu sun ce kafin karshen shekara ta 2016 za su kammala aiki da shirin da suka kaddamar, ciki har da kirkirar wani asusu na miliyoyi dubbai na Euro.

https://p.dw.com/p/1H4sr
Malta EU Afrika Gipfel Abschluss-PK
Hoto: Reuters/D. Z. Lupi

Shugabanninn kungiyar tarayyar Turai EU sun alkawarta samar da kudi wuri na gugan wuri Euro miliyan dubu daya ga wani asusun kungiyar EU domin aiwatar da matakan da ke cikin wani shirin magance matsalar kwararar bakin haure daga Afirka zuwa Turai. Shugaban majalisar shawara ta kasashen Turai Donald Tusk ya fada wa wani taron manema labarai a karshen taron kolin EU da shugabannin kasashen Afirka kan 'yan gudun hijira a tsibirin Malta.

"Za mu kaddamar da ayyukan da za su inganta damarmakin samun aikin yi a yankunan asali da kuma yankunan da bakin haure ke yada zango a ciki da ke gabaci da arewaci da yammacin Afirka a hanyarsu ta zuwa Turai. An tsara wannan shirin ne domin magance matsalar yin kaurar tun daga tushe da inganta hadin kai a batun da ya shafi yin kaura ta halal."

Matsalar 'yan gudun hijirar dai ta shafi dukkan nahiyoyin Turai da Afirka, a saboda haka ne a cewar shugaban hukumar tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ya zama wajibi tarayyar Turan ta taimaka wa kasashen Afirkan musamman yankunan da aka fi fama da rikici.

Malta EU-Afrika-Gipfel in Valletta
Turai ta bayar da tallafi mai tsoka na Horas da matasan AfirkaHoto: Reuters//D. Z. Lupi

"Tattaunawar sun gudana cikin yanayi na mutunta juna. Matsala iri guda ake fuskanta a bangarori biyu na tekun Bahar Rum, kuma dole ne mu taimaka wa 'yan Afirka domin matsalar da suke fuskanta ta fi ta mu girma."

Wannan taron shi ne irin shi na farko.

Wannan taron kolin tsakanin Afirka da Turai na zama irin shi na farko kan 'yan gudun hijira da bakin haure da ya gudana tsakanin manyan shugabannin sassa guda biyu. An kuma fi mayar da hankali kan shugabannin yayin da kuwa akwai mahalarta taron da ke aiki ba ji ba gani a bayan fage, musamman wadanda suka yi taron sharen fage na tsawon sa'o'i 20, taron kuma da yayi nasara inji Eloge-Armand Issa-Gadenga daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

"Hakika mun kasance cikin wani wadi na tsaka mai wuya. Matsayin 'yan Afirka ya sha bambam da na Turawan. Amma daga wani mizanin dole kowa ya sassauto."

A karshe dai an cimma daidaito, inda mahalarta taron suka daidata kan karin kudi ga nahiyar Afirka, wadda ita kuma daga bangarenta za ta gaggauta sake karbar bakin hauren, abin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana da wani sabon babi na hadin kai tsakanin Turai da Afirka.

"Manufa ita ce yaki da matsalar bakin haure. Hakan zai yiwu ne idan aka samu kyakkyawan shugabanci a Afirka tare da kara shigar da kungiyoyin farar hula cikin aikin. da kuma samar wa matasa kyakkyawan makoma. Asusun tarayyar Turai zai taka rawa bisa manufa, haka nan ma Jamus za ta yi amfani da hulda tsakaninta da daidaikun kasashen Afirka don cimma manufa."

Tallafin Euro miliyan dubu dayan dai kari ne ga taimakon raya kasa kusan Euro miliyan dubu 20 da EU ke bai wa Afirka.