1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka a Jaridun Jamus

Sharhunan Jaridun Jamus game da nahiyar Afirka

default

Kamfen yaƙi da cutar AIDS a Botswana

Paparoma a Afirka / Sudan / Rikicin tattalin arziki

Ko da yake a wannan makon bulaguron shugaba El-Bashir na ƙasar Sudan zuwa ƙasashe maƙobta don neman goyan baya a taƙaddama tsakaninsa da kotun duniya akan miyagun laifuka shi ne ya fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus, amma duk da haka sun leƙa yankuna daban-daban na Afurka domin duba irin wainar da ake toyawa a fannoni na siyasa da tattalin arziki. Misali jaridar Berliner Zeitung, wadda tayi sharhi akan ziyarar Paparoma Benedikt na 16 ta farko a nahiyar Afurka inda take cewar:

Paparoma a Afirka

Ein afrikanischer Geistlicher begrüßt den Papst

Paparoma Benedikt na 16 lokacin ziyararsa a Kamaru

"Duk da ƙorafe-ƙorafen da ake yi a game da adawar da Paparoma Benedikt na 16 ya nunar ga amfani da kororon roba, wadda take da muhimmanci wajen yaƙi da yaɗuwar cutar Aids, amma fa abin lura a nan shi ne ra'ayinsa ra'ayi ne dake da nasaba da addini, musamman ma mujami'ar katolika, ba shi da wata dangantaka da manufofin siyasa ko matakan kiwon lafiya. Kuma a nan ne take ƙasa tana dabo, inda aka kasa banbanta manufofi na siyasa da manufofi na addini."

Sudan

Omar Hassan Ahmad al-Bashir Präsident Sudan Internationalen Strafgerichtshof Logo

Shugaban Sudan Omar Hassan Ahmad al-Bashir

A wani mataki na fatali da zartaswar kotun ƙasa da ƙasa akan miyagun laifuka a wannan makon shugaba El-Bashir na ƙasar Sudan ya kai ziyara ƙasashe maƙobta, daga ciki kuwa har da ƙasar Masar. A lokacin da take ba da rahoto game da haka, jaridar Süddeutsche Zeitung ta ambaci ma'aikatar harkokin wajen Sudan tana mai faɗi cewar:

"Tare da wannan ziyara shugaba El-Bashir na fatan bayyana wa kotun ƙasa da ƙasa dake birnin The Hague ne cewar ba ta da sauran martaba a idanunsa. Ita dai ƙasar Masar bata da wakilci a kotun ta kuma yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya da ya sake sammacen da kotun tayi wa El-Bashir. Bisa ga ra'ayin gwamnatocin ƙasashen Larabawa ma dai ƙasashen yamma na amfani da kotun ne don danniya kawai. Kuma ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Larabawa ta fito fili tayi Allah Waddai da wannan sammace akan shugaban ƙasar Sudan."

Tasirin matsalar tattalin arzikin duniya a Afirka

Symbolbild Finanzkrise Finanzinvestoren Heuschrecken

Rikicin kuɗi a duniya

Bisa ga dukkannin alamu tasirin rikicin kuɗi na duniya ya fara nuna tasirinsa akan ƙasashen Afurka sakamakon faɗuwar farashin ɗanyun kayayyaki a kasuwannin duniya, a cewar jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, wadda ta ƙara da cewar:

"Da farkon fari dai an yi zaton cewar rikicin kuɗin da ake fama da shi a duniya ba zai rutsa da ƙasashen Afurka ba, saboda ƙasashen ba su taka wata muhimmiyar rawa a kasuwar hada-hadar kuɗi ta ƙasa da ƙasa. Amma fa a yanzun murna na neman komawa ciki domin kuwa a sakamakon wannan rikici da koma bayan tattalin arzki farashin ɗanyun kayayyakin da ƙasashen na Afurka suka dogara akai don samun kuɗaɗen shiga ya taɓarɓare ta yadda guguwar rikicin a yanzun ta rutsa da wannan nahiya. A wasu ƙasashen ma tuni aka dakatar da aikin haƙar ma'adinai saboda kwalliyar ba zata iya mayar da kuɗin sabulu ba."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal