1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

March 21, 2009

Sharhunan jaridun Jamus game da nahiyar Afirka

https://p.dw.com/p/HGoU
Paparoma Benedikt na 16 a Yawunde, KamaruHoto: AP

Paparoma a Afirka/Madagaska

A wannan makon mai ƙarewa dai, ziyarar Paparoma Benedikt na 16 ga ƙasashen Afurka ita ce ta fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridu da mujallun Jamus, sai kuma halin da ake ciki a Madagaskar, inda a wannan makon sojoji suka ƙwace ragamar mulki daga hannun shugaba mai ci Ravalomanana domin danƙa wa abokin hamayyarsa Andry Rajoelina. Amma da farko zamu fara ne da sharhin da jaridar Berliner Zeitung ta rubuta dangane da ziyara ta farko da Paparoma Benedikt na 16 ya kai nahiyar Afurka. Jaridar dai cewa tayi:

Angola Vatikan Papst Benedikt in Luanda Frauen auf der Straße
Gagarumar tarba ga Paparoma a AngolaHoto: AP

Ziyarar Paparoma a Afirka

"Babban manufar wannan ziyarar dai ita ce domin kare matsayin da mujami'ar Katolika take da shi a nahiyar Afurka. Domin kuwa a halin da ake ciki yanzun 'yan ƙananan ɗariƙu na kirista sai daɗa samun magoya baya suke fiye da mujami'ar Katolika. Dalilin haka kuwa shi ne cakuɗa kiristanci da al'adun garjaiya na Afurka da waɗannan ɗarƙu suke yi. Mabiya ɗariƙar Katolika na sa ran samun taimako domin tinkarar matsalolinsu na rayuwa ta yau da kullum. Amma fa tun akan hanyarsa a cikin jirgin sama Paparoma ya ce kororon roba, ba shi ne zai taimaka a magance matsalar yaɗuwar cutar Aids ba, lamarin da a lokaci guda manazarta ke ganin wani mataki ne na fatali da shirin ƙayyade yawan haifuwa."

Cutar Aids a Afirka

Aids in Südafrika
Hoto: picture-alliance / dpa/dpaweb

Ita ma jaridar Die Tageszeitung a cikin sharhinta ɗorawa tayi akan wannan batu, inda take cewa:

"Hattara fa, ana fuskantar barazanar salwantar rayukan miliyoyin mutane a yankin kudancin Afurka. Domin kuwa bayanai sun nuna cewar kimanin mutane miliyan 22 ne ke ɗauke da ƙwayar cutar HIV mai karya garkuwar jikin ɗan Adam a yankin kudu da hamadar Sahara. Amma fa duk da wannan barazana, a ziyararsa ta farko ga nahiyar Afurka Paparoma Benedikt na 16 ya sa ƙara sanya murna ta koma ciki sakamakon gargaɗin da yayi a game da amfani da kororon roba."....Bisa ga ra'ayin jaridar dai wannan furuci babban koma baya ne a ƙoƙarin da ake yi na dakatar da yaɗuwar wannan cuta da zame wa duniya gagara badau."

Madagaska

Oppositionsführer Andry Rajoelina mit Soldaten in Antananvario, Madagaskar
Sabon shugaban Madagaska, Andry RajoelinaHoto: picture alliance/dpa

A farkon wannan makon sojoji a ƙasar Madagaskar suka karɓe ragamar mulki daga hannun shugaba mai ci Marc Ravalomanana, kuma daga baya kotun ƙoli ta ƙasar ta amince da a danƙa wa abokin gabarsa Andry Rajoelina ragamar ta mulki don dakatar da tashe-tashen hankulan dake neman rikiɗewa zuwa yaƙin basasa a tsuburin dake yankin kudu maso gabacin Afurka, a cewar jaridar Neues Deutschland, wadda a ganinta wannan goyan baya da Rajoelina ya samu daga kotun ƙolin yana da muhimmanci domin tabbatar da shi kan karagar mulki ganin irin martanin da ake samu akan matakin na soji daga dukkan sassa na duniya."

Mawallafi: Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal