Afirka a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 28.02.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka a Jaridun Jamus

Sharhunan Jaridun Jamus game da nahiyar Afirka

default

Shugaban Kenya Mwai Kibaki

Kenya/Sudan/Zimbabwe

To a wannan makon ma dai kamar a makon da ya gabata jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni masu tarin yawa akan al'amuran Afurka, kama daga halin da ake ciki a Kenya zuwa Sudan da Zimbabwe. A can ƙasar Kenya dai wata mummunar taɓargaza ce aka fallasa a game da ta'asar 'yan sandan ƙasar sakamakon wani bincike da majalisar ɗinkin duniya ta gudanar. A lokacin da take gabatar da rahoto akan haka, jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

Kenya

"Kimanin gawawwakin mutane 500 aka gano a wasu dazuzzukan dake kewayen birnin Nairobi, waɗanda kuraye suka yi kaca-kaca da su tsakanin yuni da oktoban shekara ta 2007. Wasu daga cikin gawawwakin kuma an gano harbin albarushi a kawunansu, kuma 'yan sandan ƙasar Kenya ne ke da alhakin wannan mummunar ta'asa. Galibin matattun kuma membobin wata kungiya ce da addini mai laƙabin mafise. Babban abin da ake zargin 'yan sandan kenya da shi shi ne kasancewar suna aiwatar da kashe-kashen ne a bisa wani tsayayyen tsari kuma manyan jami'an 'yan sanda da na siyasa na da hannu dumudumu a ciki."

UN AU Hybridmission in Darfur

Sudan

Ana ci gaba da tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan tawayen lardin Darfur na kasar Sudan a Katar, kuma wata yarjejeniyar da sassan biyu suka sa mata hannu na mai yin nuni da kyakkyawar niyyar sassan biyu na dakatar da rikicinsu, a cewar jaridar Neues Deutschland. Ta kuma ƙara da cewar:


"Ita kanta gwamnatin Sudan tana sha'awar ganin an ci gaba da wannan tattaunawa, musamman ganin cewar nan ba da daɗewa ba ne kotun ƙasa-da-ƙasa akan miyagun laifukan yaƙi zata tsayar da shawara a game da yiwuwar ɗaukaka ƙara akan shugaba Umar El-Bashir a game da ta'asar yaƙin Darfur. Nuna kyakkyawar niyya game da warware rikicin a cikin ruwan sanyi daga ɓangaren gwamnati zai taimaka alƙalan kotun su nuna sassauci a hukuncin da zasu yanke."

Robert Mugabe November 2008

Zimbabwe

Har yau ƙasar Zimbabwe na fama da cutar kwalera a yayinda ake fama da ƙarancin magunguna a asibitocin ƙasar. A lokacin da take gabatar da rahoto akan haka jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:

"A makon da ya gabata ne shugaba Mugabe yayi bikin samun shekaru 85 da haifuwa. Kuma kamar yadda aka saba a liyafar ta bana ma sai da aka yi facaka, inda a baya da samfuran barasa iri daban-daban aka shigo da tan-tan na kifi da kuma shanu saba'in da shida. An gudanar da wannan biki a daidai lokacin da cutar kwalera ke ci gaba da yaɗuwa tsakanin al'umar Zimbabwe, wadda aka ce ita ce mafi muni da aka taɓa gani a cikin tarihi, a nahiyar Afurka. Cutar ta halaka mutane dubu huɗu a yayinda wasu sama da dubu 100 ke ci gaba da fama da ita. Ta la'akari da haka sabuwar gwamnatin da aka naɗa tare da Morgan Tsvangirai a matsayin Piraminista tana da jan aiki gabanta."


A. Tijani Lawal