Afirka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 04.02.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka A Jaridun Jamus

Sharhunan jaridun Jamus game da nahiyar Afirka

default

Gangamin zanga-zanga a Madagaskar

Madagaskar/Lampedusa/Zimbabwe

Madagaskar

Da farko zamu fara ne da yada zango a tsuburin Madagaskar, wanda a wannan makon ya sha fama da tashintashinar siyasa wadda tayi sanadiyyar rayukan mutane masu tarin yawa a fadar mulki ta Antananarivo. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta rahoto tana mai cewar:

"Ainihin musabbabin wannan tashintashina da hargitsin siyasa shi ne rashin gamsuwar al'umar ƙasar da salon mulkin shugaba Ravalomanana dangane da hauhawar farashin kayan masarufi da man fetur. Ravalomanana yayi fatali da manufar karya farashin kayan masarufin yana mai imanin cewar barin kasuwa tayi halinta zai taimaka al'amura su daidaita. Bayan sake zaɓensa da aka yi a shekara ta 2006 ya gabatar da wani shirin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa da zai taimaka a magance matsalar talauci a ƙasar a cikin shekaru biyar kacal. To sai dai kuma kawo yanzu, wannan shiri, wanda ya sha yabo daga sassan duniya daban-daban, bai tsinana kome ba inda har yau sama da kashi 70% na al'umar Madagaskar su miliyan 21 ke fama da mummunan talauci."

Lampedusa

Flüchtlingslager in Lampedusa

´Yan gudun hijira a Lampedusa

Har yau ana ci gaba da fama da tuttuɗowar 'yan gudun hijira na ƙasashen Afurka zuwa nahiyar Turai, inda al'amura ke dada yin tsamari a tsuburin Lampedusa na ƙasar Italiya, jaridar Berlin Zeitung ta bayyana ra'ayinta game da wannan ci gaba tana mai cewar:

"Abin dake faruwa a tsuburin Lampedusa na ƙasar Italiya dake tekun Baharrum, ba shakka yana kada zuciya, kuma 'yan gudun hijira na Afurka da aka tsugunar a sansanonin da aka tanadar musu a tsuburin suna cikin mawuyacin hali na kaka-nika-yi. Duk da tsauraran matakai na tsaro da ake ɗauka ana ci gaba da samun ƙaruwar 'yan gudun hijira na Afurka dake bi ta wannan hanya mai haɗarin gaske domin shigowa nahiyar Turai. Ta la'akari da haka bai zama abin mamaki ba kasancewar ƙasar ta Italiya na matsin lambar ganin an ɗauki wani mataki bai ɗaya tsakanin illahirin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai don neman bakin zaren warware wannan matsala."

Zimbabwe

Zimbabwe Cholera Patienten

Masu fama da cutar kwalera a Zimbabwe

Ƙasashen kudancin Afurka sun tashi haiƙan wajen shawo kan rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a Zimbabwe, inda suka gabatar da wani shirin warware rikicin bisa manufa, in ji jaridar Die Tageszeitung, wadda ta ƙara da cewar:

"Sai dai kuma a daidai lokacin da ake shirye-shiryen shiga shawarwarin neman kusantar juna tsakanin sassan da rikicin Zimbabwen ya shafa a Pretoriyar Afurka ta Kudu, wanda kuma daga bisani bai haifar da wani sakamako na a zo a gani ba, ƙungiyar tarayyar Turai ta ƙara tsaurara matakanta na takunkumi akan wakilan gwamnatin Zimbabwe da kuma wasu kamfanonin dake dangantaka da su a nahiyar Turai. Amma a nasu ɓangaren ƙasashen kudancin Afurka sun ki amincewa da su ƙaƙaba wa maƙobciyar tasu takunkumi. Domin kuwa yankin gaba ɗayansa ya fara jin raɗaɗin taɓarɓarewar tattalin arzikin Zimbabwen mai fama da bala'in cutar kwalera dake neman zama ruwan dare a shiyyar baki ɗaya."