Afirka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 16.01.2009
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka A Jaridun Jamus

Sharhunan Jaridun Jamus akan Afirka

default

Jacob Zuma shugaban ANC

Afirka Ta Kudu/Kongo/Somalia/Ghana

Afirka Ta Kudu

A yau za mu fara ne da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta rubuta rahoto game da yiwuwar sake gurfanar da shugaban jam´iyar ANC a Afirka Ta Kudu wato Jacob Zuma gaban shari´a. A rahoton mai taken kotun ƙolin Afirka Ta Kudu ta amince a sake yiwa Zuma shari´a jaridar ta fara ne da cewa ana iya sake gurfanar da Jacob Zuma gaban koliya dangane da zargin karɓar rashawa, to amma hakan ba zai sa ANC ta canja shawarar da yanke ta tsayar da Zuma a matsayin ɗan takararta a zaɓen shugaban ƙasar dake tafe a wannan shekara ba. Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi tsokaci kan wannan batu tana mai cewa shekara guda kafin gasar ci kofin ƙwallon ƙafa na duniya da za a yi a Afirka Ta Kudu ƙasar ta doshi hanyar shiga dambarwar siyasa. Gwamnati tana ƙara shan matsin lamba kan yadda za ta inganta matsayin rayuwar talakawa sannan ta daƙile miyagun ayyukan da suka zama ruwan dare a cikin ƙasar. Ta ce dole Afirka Ta Kudu ta gano hanyoyin da za ta rage giɓi tsakanin talakawa da masu hannu da shuni da kuma janyo hankalin masu zuba jari. Saboda haka ƙasar na buƙatar wani shugaba wanda ke da goyon bayan al´umomin ƙasar baki ɗaya.

Kongo

Jean Pierre Bemba

Jean-Pierre Bemba

Ita kuwa jaridar Tageszeitung rahoto ta buga game da zaman shari´a da kotun ƙasa da ƙasa dake birnin The Hague ta fara yiwa tsohon mataimakin shugaban Jamhuriyar Demoƙuraɗiyya Kongo Jean-Pierre Bemba. Ta ce a ranar Litinin Bemba ya gurfana gaban alƙalai inda ya saurari zargin da ake masa na aikata laifukan yaƙi. Jaridar ta ce wannan zaman ba shari´a ba ce illa kawai tabbatar da sahihancin zargin da ake masa.

Somalia

Somalia Kämpfe in Mogadishu Hawiye-Clan

Madugan haulolin yaƙi suna dako, wannan dai shi ne taken rahoton jaridar Süddeutsche Zeitung game da janye dakarun Ethiopia daga Somalia. Ta ce yanzu ragamar tabbatar da tsaro za ta koma hannun wani rukuni na sojojin Somalia da wasu sojojin sa kai na musulmi masu sassaucin ra´ayi. To sai dai rashin ga maciji dake tsakanin sojojin sa kan ka iya sa murna ta koma ciki.

Ghana

Kofi Annan Kenia Gewalt Wahl

Kofi Annan

Kofi Annan ya ceto Ghana daga faɗawa rikicin ƙabilanci inji jaridar Tageszeitung tana mai nuni da ƙoƙarin da tsohon babban sakataren na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi na ganin zaɓen da aka gudanar a ƙasar Ghana ya tafi salin-alim. Ta ce a lokacin da aka rantsar da sabon shugaban Ghana John Evans Atta Mills a ranar Laraba da ta gabata, ba wanda ya kai Kofi Annan farin ciki da nuna gamsuwa bisa dalilan cewa babban baƙon a gun bukin shi ne ya kai gwauro ya kai mari don kaucewa shiga wani rikici a Ghana kamar yadda abin ya kasance bara a Kenya bayan zaɓen wannan ƙasa.

Sauti da bidiyo akan labarin

 • Kwanan wata 16.01.2009
 • Mawallafi Mohammad Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/GZyW
 • Kwanan wata 16.01.2009
 • Mawallafi Mohammad Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/GZyW