1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka a Jaridun Jamus

Mohammad AwalDecember 6, 2008

Jaridun sun fi mayar da hankali kan rikicin garin Jos.

https://p.dw.com/p/GAl6
Masu tserewa rikicin addini a garin JosHoto: AP

A wannan makon jaridu sun fi mayar da hankali ne akan rikicin siyasa da ya rikiɗe ya zama na addini a garin Jos na jihar Filaton tarayyar Nijeriya ne sai kuma halin da ake ciki a Zimbabwe sakamakon ɓarkewar cutar kwalera.

A rahotonta jaridar Süddeutsche Zietung ta fara ne da cewa ɗaruruwan mutane sun rasu a tashe tashen hankula a Nijeriya yayin da wasu dubbai suka tsere daga gidajensu. Ta ce an ƙone gidaje da wuraren ibada a ƙarshen mako sakamakon hargitsin da ya biyo bayan zaɓen ƙananan hukumomi a Jos mai tazarar kilomita 300 arewa maso gabashin babban birnin tarayya Abuja. Ta ce a garin Jos ba riicin addini kaɗai ake fama da shi ba. Tun shekaru masu yawa da suka wuce ake taƙaddama game da mallakar dukiya.

Ita ma a rahotonta jaridar Tageszeitung cewa ta yi maƙwabta sun yi ta kaiwa juna hari da makaman zamani da na gargajiya. Ta ce bisa ga dukkan alamu an shirya ta da zaune tsaye ne domin tun gabanin bayyana sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin ´yan banga suka fara bankawa wuraren ibada wuta suna kai hari kan duk wani abu mai motsi. Ta ce a Jos kamar a wasu sassa na tarayyar Nijeriya ana fama da rikicin ƙabilanci da na siyasa yayin da su kuma ´yan siyasa ke amfani da wannan saɓanin da har yanzu aka kasa gano bakin zarenw arware shi, don cimma burinsu.

Tashin hankali tsakanin Kiristoci da Musulmai taken rahoton da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta kenan game da rikicin na Jos. Ta ce ana iya danganta wannan hargitsi da gwagwarmayar mallakar dukiya fiye da addini. Ta ce yanzu dai alhaki na kan shugabanni da su ci-gaba da neman bakin zaren warware rikice-rikicen ƙabilanci da na addini da suka zamewa Nijeriya ƙayar kifi a wuya.

Annobar kwalera a Zimbabwe, kanun labaran jaridar Tageszeitung kenan kan mawuyacin halin da ake ciki a wannan ƙasa da ke kudancin Afirka. Jaridar ta rawaito Hukumar Lafiya ta Duniya WHO na cewa kimanin mutane 500 suka rasa rayukansu sakamakon wannan annoba ta cutar kwalera a Zimbabwe amma ƙungiyoyin kare haƙin bil Adama sun ƙiyasce cewa waɗanda suka mutu sun kai mutum 1000. Jaridar ta ce tattalin arziki da tsarin kiwon lafiya a Zimbabwe sun ruguje gaba ki ɗaya ƙarƙashin mulkin kama karya na shugaba Robert Mugabe.

Yanzu kuma sai Kongo inda har wa yau jaridar Tageszeitung ta rawaito firiministan kasar belgium yves Leterme yana mai tabbatar da kiran da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi masa na tura dakarun ƙasarsa Janhuriyar Demoƙuraɗiyya Kongo a wani aikin wucin gadi na taimakawa dakarun ƙasa da ƙasa a gabashin Kongo. To sai dai daga birnin Brussels rahotanni na nuni a cewa gwamnati za ta amsa wannan kira ne bisa sharaɗij cewa wasu ƙasashen Turai za su ba da gudunmawar sojoji.

An yi ƙarar wasu shugabannin Afirka, inji jaridar Frankfurter Rundschau tana mai nuni da zargin da ƙungiyar Transparency International ta yi cewa shugaba Omar Bango na Gabon da Denis Sassou Nguesso na Kongo Brazaville da kuma Teodoro Obiang Nguema na Equitorila Gini sun yi amfani da dukiyar ƙasa da suka sata wajen sayen ƙasaitattun gidaje a Faransa. To sai dai a bara ma ƙungiyar ta yi ƙarar wasu shugabannin Afirka amma har yanzu ba a ja kunnensu ba.