1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka a Jaridun Jamus

Mohammad AwalNovember 30, 2008

A wannan makon mai ƙarewa ma dai jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne kan matsalar fashin jiragen ruwa a Somalia.

https://p.dw.com/p/G67B
Fashin jiragen ruwa a SomaliaHoto: picture-alliance/ dpa

A rahoton da ta rubuta kan wannan batu jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rawaito ƙungiyar tarayyar Turai na mai shirye shiryen aikewa da jiragen ruwan yaƙi da fatattakar ´yan fashin jirgin ruwa a Somalia. Ta ce yanzu dai shirye-shirye a birnin Brussels sun yi nisa inda ƙungiyar za ta karɓi ragamar wannan aiki daga ƙungiyar NATO wadda a cikin makonnin baya bayan nan ta samu ƙarin darasi wajen yaƙi da ´yan fashin jirgin ruwa. To sai dai jaridar ta rawaito NATO na cewa matsalar ba ta yi tsanani kamar yadda ake yayatawa ba domin a cikin wannan shekara jiragen ruwa 97 daga cikin dubu 16 da suka ratsa ta ruwayen gaɓar tekun Somalia ake yi fashinsu, wato kenan bai kai kashi ɗaya cikin 100 ba.

Sojojin Jamus 1400 za su fatattaki ´yan fashin jiragen ruwa, wannan shi ne taken rahoton jiragen Süddeutsche Zeitung, inda ta rawaito majiyoyin gwamnatin ƙasar na cewa wannan shi ne yawan sojoji da Jamus za ta bayar ga rundunar da ƙungiyar EU ke shirin haɗawa don yaƙi da ´yan fashin. Ta ce ƙasar kuma na shirin ba da wani jirgin ruwan yaƙinta da yanzu yake Masar don tafiyar da wannan aiki da aka yiwa laƙabi da Atalanta.

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung ta mayar da hankali ne kan ƙasar Zimbabwe inda ta rawaito ministan ƙasar Botsawana Phandu Skelemani a matsayin wani ministan wata ƙasar Afirka ta farko da ya yi kira da a ƙaƙabawa gwamnatin Zimbabwe takunkumi. Jaridar ta ce ganin har yanzu duk ƙoƙarin da aka yi na sasantawa ya ci-tura to lokaci ya yi da ya kamata a ɗauki irin wannan mataki kan shugaba Robert Mugabe don matsa masa lamba ya sassauto.

Dakarun gwamnatin na aikata tarzoma a Kongo amma duniya tana kyau da kai, wannan dai shi ne taken rahoton da jaridar Tageszeitung ta rubuta tana mai yin nuni da zargin da ƙungiyar kare haƙin bil Adama ta Huma Rights Watch ta yi cewa zaɓaɓɓiyar gwamnatin Kongo na yiwa ´yan adawa kisan gilla da cin zarafinsu. Jaridar ta ce sabon abu a cikin wannan zargi shi ne akwai hannun shugabannin hukumomin tsaron ƙasar a cikin wannan ta´asa, inda daga watan Agustan shekara ta 2006 zuwa watan Mayun wannan shekara dogarawan fadar shugaba Kabila sun yiwa aƙalla mutane 125 kisan gilla ko kuma sun sa an ɓatar da su. Jaridar ta ce yayin da ake mayar da hankali kan rikicin ´yan tawaye a gabashin Kongo bai kamata a yi watsi da abubuwan da ke faruwa a yammacin ƙasar ba. Ta yi kira ga ƙasashen dake ba da tallafi da su taimaka a kafa wata hukumar shari´a mai zaman kanta da samar da sahihiyar majalisar dokoki da sauran hukumomin demoƙuraɗiyya a Kongo.

A yau za mu kammala ne da wani rahoton jaridar Süddeutsche Zeitung ta na mai cewa tsohon sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan zai zama babban mai hasashen yanayi a Afirka. Jaridar ta jiyo mista Annan na cewa zai bari a kakkafa tashoshin hasashen yanayi kimanin 5000 a ilahirin nahiyar Afirka don tara bayanai game da yanayin wannan nahiya. Manufa shi ne wayarwa da manoma kai game da yanayi, musamman yanzu da ake fama da matsalar sauyin yanayi wanda ke barazana ga aikin noma.