Afirka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 24.11.2008
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka A Jaridun Jamus

Fashin jiragen ruwa a ga ɓar tekun Somalia ya fi ɗaukar hankalin jaridun.

default

Jirgin ruwan ɗaukar mai na Saudiyya da aka yi fashinsa.

A wannan makon mai karewa dai jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne akan masifar fashin jiragen ruwa a tekun Aiden dake da ƙasar Somalia, sai kuma halin da ake ciki a Kongo. A rahotonta mai taken harkar mai riba a gaɓar tekun Somalia jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta fara ne da cewa bisa ga dukkan alamu yanzu akwai ´yan fashin jiragen ruwa fiye da 1000 a wannan yanki dake zama ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jiragen ruwa ga cinikaiya tsakanin ƙasa da ƙasa. Ta ce yanzu haka wannan yanki ya zama wata sabuwar gaɓar teku ga ɓarayin jirgin ruwa waɗanda suka faɗaɗa yankin da suke aikata wannan ta´asa ya zuwa cikin tekun Indiya ta amfani da sabbin fasahohi na zamani.

Ita kuwa a rahotonta jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi ´yan fashin jiragen ruwa na ƙara yin ƙarfi. Ta ce bisa ga dukkan alamu kasancewar jiragen ruwan yaƙin ƙasashen duniya a wannan yankin ba ta wani tasiri ga ´yan fashin jirgin ruwa a yankin ƙahon Afirka. Ta ce bayan fashin wani katafaren jirgin ruwan ɗaukar mai na Saudiya, kafin ranar Laraba an sake yin fashin wasu jiragen ruwa. Hakan wani ƙalubalae ne ga ƙasashe duniya da su tashi tsaye su ɗauki matakai yaƙi da wannan aika-aika kana kuma a yi ƙoƙarin kafa sahihiyar gwamnati a Somalia.

Jamus za ta shiga cikin aikin yaƙi da masu fashin jiragen ruwa a gaɓar tekun Somalia, wannan dai shi ne taken rahoton da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta rubuta inda ta ƙara da cewa bayan ƙuduri da ministocin harkokin wajen ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai suka yanke na yaƙi da masu fashin jiragen ruwa, wata muhawwara ta taso a Jamus kan yadda za a fara wannan aiki. Jaridar ta rawaito wakilan gwamnatin ƙawance na nuna amincewarsu da shigar da dakarun Jamus a wannan aiki.

´Yan tawaye magoya bayan Janar Nkunda sun janye daga wasu yankuna na gabashin Kongo, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung. To sai dai wannan janyewa ba ta shafi filin daga dake kudancin lardin Kivu ta Arewa ba, wani yanki mai tazarar kilomita 15 daga garin Goma. Jaridar ta ce bayan ganawa da yayi da wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman ga Kongo, wato tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo, Nkunda ya amince ya janye dakarunsa a wani mataki na nuna kyakkyawar aniyar samun zaman lafiya. To sai dai kuma a lokaci ɗaya Nkunda ya jaddada bukatarsa ta soke dukkan yarjeninoyi da gwamnati ta ƙulla da China waɗanda kuɗinsu ya kai dala miliyan dubu 10.

Ita kuwa jaridar Die Welt ta yi nuni ne da roƙon da ke fitowa daga gabashin Kongo na aikewa da dakarun tarayyar Turai yanki don tallafawa dakarun ƙawance na tarayyar Afirka da MƊD.

Yayin da Jamus ta miƙa jami´ar Rwanda Rose kabuye ga hukumomin Faransa, ´yan Rwanda sun gudanar da zanga-zangar yin tir da wannan mataki da Jamus ta ɗauka. Jaridar ta ce gangamin da mutane kimanin dubu 500 suka yi a Kigali babban birnin ƙasar shi ne mafi girma da aka taɓa gudanarwa a cikin ƙasar.

 • Kwanan wata 24.11.2008
 • Mawallafi Mohammad Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/G1HS
 • Kwanan wata 24.11.2008
 • Mawallafi Mohammad Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/G1HS