Afirka A jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 30.08.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka A jaridun Jamus

Jaridun sun mayar da hankali kan batutuwa da dama a nahiyarmu ta Afirka

default

Mugabe a faretin girmamawa yayin buɗe zaman majalisa a birnin Harare

Jama´a barkanku da warhaka. A shirin na yau za mu fara da ƙasar Ghana inda a ranar Laraba da ta gabata aka kammala taron majalisar ɗinkin duniya game da sauyin yanayi. A sharhin da ta rubuta jaridar Tageszeitung cewa an samu ƙwarya-ƙwaryan ci-gaba a taron inda aka samu kusantar juna tsakanin ƙasashe masu arziiin masana´antu da ƙasashe masu tasowa duk da taƙaddamar da suke yi dangane da kuɗi da matakan kare dazuzzuka. Duk da cewa ba a cimma wata yarjejeniya ba dangane da muhimman batutuwa a taron na birnin Accra, amma jarida ta ci-gaba da cewa a jawaban da suka yi mahalarta taron sun ba da la´akari da shawarwarin da takwarorinsu suka bayar maimakon dagewa kan matsayinsu. Ta ce yanzu ya rage a daidaita dangane da ka´idojin sabuwar yarjejeniyar kare muhalli da za a tattauna kai a gun taron ƙolin ƙasashen duniya kan sauyin yanayi da zai gudana a garin Posen na ƙasar Poland a farkon watan Disamban, wadda za a amince da ita a taron birnin Kopenhagen a baɗi idan Allah Ya kaimu.

An yiwa shugaban Zimbabwe Robert Mugabe kuwa a zaman majalisar dokoki inda aka zaɓi na jam´iyar adawa ta MDC Lovermore Moyo a matsayin kakakin majalisar. Wannan dai shi ne taken rahoton da Neue Zürcher Zeitung ta rubuta tana mai nuni da jawabin buɗe zaman majalisar da shugaban na Zimbabwe yayi a ranar Talata a gaban wakilai da aka zaɓa a zaɓen da ya gudana a cikin watan Maris. Wakilan ´yan adawa na masu ra´ayin cewa zaman majalisar a saɓa da yarjejeniyar da suka cimma a ranar 21 ga watan Yuli wadda a cikin jam´iyun suka amince da cewa ba za a kafa wata doka ba har sai an ga makwancin tattaunawar da ake da zumar kafa gwamnatin raba madafun iko.

Harbe harbe ya sa an daina ba da taimakon abinci a Darfur, inji jaridar Süddeutsche Zeitung a cikin rahoton ta inda ta ce ƙazancewar tashe tashen hankula a yankin Darfur ya sa a dole ƙungiyar agaji ta Jamus ta dakatar da aikin ta a yankin dake yammacin ƙasar Sudan. Jaridar ta rawaito shugaban ƙungiyar Johann van der Kamp na mai cewa sabon yananyin da aka shiga a yankin musamman na yawaitar kai hari kan ayarin motocin jigilar kayan agajin ya sa ba za su iya ci-gaba da aikinsu a yankin ba. Wannan matakin na janye ma´aikatan agajin na Jamus zai shafi rayuwan mutane kimanin dubu 450 musamman a arewacin Darfur waɗanda suka dogara kacokan kan taimakon wannan ƙungiya.

Ita kuwa jaridar Tageszeitung ta yi tsokaci kan fashin jirgin saman Sudan da ´yan tawayen Darfur suka yi tana mai cewa yanzu yaƙin wabnnan yanki ya fara shafar sufurin jiragen sama. Ta ce sakamakon mummunan harin da dakarun tsaron Sudan suka kai kan wani sansanin ´yan gudun hijira dake kudancin Darfur ya tinzira ´yan tawayen yin fashi jirgin saman Sun Air mai zama kansa. Da farko dai waɗanda suka yi fashin Jirgin saman samfurin Boeing 737 sun so zuwa Faransa don ganawa da madugun ´yan tawayen Darfur Abdelwahid al-Nur amma a ƙarshe suka tsaya a Libya.