1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

Awal, MohammadJuly 11, 2008

Jaridun sun mayar da hankali kan alkawarin da G8 ta yiwa Afirka

https://p.dw.com/p/EagN
Mbeki da Firimiyan Japan Fukuda a taron G8 da Afirka a Toyako, Japan.Hoto: AP

Africa G8/Africa EU/Zimbabwe/Ghana

Jama´a barkanku da warhaka. A wannan mako jaridun sun fi mayar da hankali ne kan alƙawuran da ƙasashe masu arzikin masana´antu suka yiwa ƙasashen Afirka amma har yau ba a gani a ƙasa ba.

A cikin wani sharhi mai taken tallafi ga Afirka, jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi: da farko dai kamar za a yi wani abin kirki dangane da alƙawarin da ƙungiyar tarayyar Turai ta yi na taimakawa manoman Afirka da euro miliyan dubu ɗaya don sayen irin shuka da takin zamani. Inda ta so ta rage tallafin da take bawa manoma a Turai don taimakawa Afirka. Amma daga baya ya fito fili cewa duk wani taimako daga Turai taƙatacce ne kuma EU ta ci-gaba da bin manufofinta na tallafawa manomanta. Jardidar ta ce hasali ma a bara EU ta rage yawan taimakon raya ƙasa da take bawa Afirka ne. Ita kuwa a sharhinta jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rawaito roƙon da Bankin Duniya da majalisar ɗinkin duniya da kuma ƙungiyoyin agaji suka yiwa ƙungiyar G8 ne na ta ƙara yawan taimakon da take ba Afirka kana kuma ta cika alƙawuran da ta ɗauka na taimakawa nahiyar a taron ta na Gleneagles a shekara ta 2005. Jaridar ta ce rashin cika alƙawuran na barazana ga cimma muradun nan na ƙarni dangane da magance matsolin yunwa da cututtuka. Ita ma a sharhin ta akan wannan batu jaridar Tageszeitung cewa an kammala taron ƙolin G8 a tsibirin Hokkaido na ƙasar Japan ba tare da gabatar da wani ƙwaƙƙwaran shirin taimakawa Afirka ba musamman yanzu da nahiyar ke fargabar shiga wani mawuyacin hali sakamakon hauhawar farashin makamashi, kayan abinci da kuma da matsalar tsadar rayuwa.

Zai wuya a samu wata damar yin sulhu a Zimbabwe wannan dai taken rahoton da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta rubuta ke nan kan halin da ake ciki a Zimbabwe. Ta ce fatan kafa wata gwamnatin haɗin kan ƙasa a Zimbabwe na ƙara gushewa saboda ƙin da shugaba Robert Mugabe yayi na sauka daga kan kujerar shugabancin ƙasar ba. Ta ce dangane da wannan taurin kunni na Mugabe, ya sa ana nuna shakku ko ƙoƙarin shiga tsakani da shugaban Afirka ta Kudu Thabo Mbeki ke yi zai hafar da ɗa mai ido. Ita kuwa jaridar Financial Times a Jamus labari ta buga game da shirye shiryen da kamfanoni a Zimbabwe ke yi na farfaɗo da kansu bayan mulkin Mugabe. Ta ce a halin da ake ciki kamfanoni sun fara nazarin wasu sabbin tallace-tallacen nemawa Zimbabwe masu zuba jari, domin a nasu ra´ayin ƙarshen ɗan kama karyan na Zimbabwe mai shekaru 84 na ƙara ƙaratowa.

"Gagarumin shiri ga baƙin gwal." Gwamnatin Ghana ta ƙuduri aniyar ba da ɓangaren haƙar mai fifiko yayin da al´umar ƙasar ke fargabar shiga wani hali irin na Nijeriya. Wannan dai shi ne taken rahoton da jaridar Frankfurter Rundschau ta buga game da arzikin mai da aka gano a Ghana. Jaridar ta saka ayar tambaya ko shirin gwamnati na kafa wani asusun tara kuɗin man da Ghana za ta samu idan ta fara fid da mai ɗin a shekara ta 2010 zai yi nasara? Gwamnati ta ce za a yi amfani da ribar da wannan asusun zai samar wajen bawa ƙananan kamfanoni bashi. To amma saboda matsalar cin hanci da rashawa da ƙasar ke fama da ita, ba bu tabbas ko wannan shiri zai yi nasara.