Afirka a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 17.06.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka a Jaridun Jamus

Sharhunan Jarun Jamus kan Afrika

default

Somalia


Sudan/Süd Afrika/Nigeria/Somaliya

Sudan

Daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus dangane da al'amuran Afurka a wannan makon har da tsautsayin dake tattare da sufurin jiragen sama a samaniyar nahiyar ta la'akari da yawan haɗarurrukan da ake fuskanta, kamar dai wanda aka fuskanta a birnin Khartoum na kasar Sudan a wannan makon. A cikin nata sharhin jaridar Der Tagespiegel cewa tayi:

Süd Afrika

"Duk da cewar yawan zirga-zirgar jiragen sama a nahiyar Afurka bai zarce kashi uku cikin dari idan aka kwatanta da sauran sassa na duniya ba, amma fa barazana sai dada karuwa take a shawagin jiragen sama tsakanin Cape-Town ta Afurka ta Kudu da Alkahira ta Masar. Alkaluma sun nuna cewar Afurka ke da kashi 20 cikin dari na yawan hadarurukan jiragen sama a duniya. Daga cikin ummalaba'isin hadarrukan kuwa har da rashin kulawar mahukunta da yi wa ka'idojin shawagin jiragen rikon sakainar kashi da kuma rashin gyara yadda ya kamata. Hakan ta kai ga Kungiyar Tarayyar Turai ta saka kamfanonin jiragen saman Afurka 85 a cikin jerin masu fama da tsautsayi a misalin shekaru biyun da suka wuce."

Nigeria

Ita kuwa jaridar kasuwanci ta Handelsblatt cewa tayi:

"Nijeriya ce ta fi kaurin suna wajen yi wa al'amuran tsaron sufurin jiragen sama rikon sakainar kashi a tsakanin kasashen Afurka. A bayan wasu jerin hadarurukan jiragen saman da aka sha famar fuskanta a cikin shekara ta 2005, a kuma baya-bayan nan an fuskanci wasu hadarurukan guda biyu a Nijeriyar, mai yawan mutane sama da miliyan dari da arba'in. To sai dai kuma akalla bayanai na hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta kasa da kasa LATA a takaice sun ce akwai kyakkyawar niyya a zukatan jami'an siyasar kasar game da yin gyara ga lamarin."

Afrika

Kasashen Asiya ne kawai zasu iya samar da ci gaba mai ma'ana a nahiyar Afurka. Wannan ra'ayin, jaridar Rheinischer Merkur ce ke dauke da shi, ta kuma kara da cewar:

"A yanzu haka dai dangantakar tattalin arziki tsakanin Afurka da Asiya ta kankama matuka ainun fiye da zamanin baya, musamman ma kasar China, inda aka samu ribanyar yawan abin da kasashen Afurka ke fitarwa zuwa Chinar da misalin kashi 48 cikin dari tsakanin shekara ta 2000 da shekara ta 2005. Wannan habaka da aka samu a cinikayya tare da makekiyar kasar ta Asiya ka iya zama wata kyakkyawar dama ga ci gaban nahiyar Afurka. Domin kuwa ta haka kasashen Afurka zasu samu wata kafa ta taka rawar gani a kasuwannin duniya, saboda da yawa daga cikin kamfanonin kasar China dake zuba jari a Afurka na taka muhimmiyar rawa a gasar ciniki ta kasa da kasa."

Somaliya

A kasar Somaliya, wadda rikicinta ya ki ci ya ki cinyewa, masu tsananin akidar addini sun ki sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta domin ba wa Majalisar unkin Duniya damar tura sojan kiyaye zaman lafiya zuwa kasar ta gabacin Afurka. A lokacin da take ba da rahoto akan haka jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:

"A makon da ya gabata ne tawagar wakilan kwamitin sulhu na MDD suka gana da gaggan jami'an siyasar kasar Somaliya a makobciyar kasa ta Djibouti domin tattauna maganar tsugunar da sojan kiyaye zaman lafiyar majalisar bisa sharadin cimma wata tsayayyar yarjejeniya ta tsagaita wuta da kuma janyewar sojan kasar Habasha a cikin kwanaki 120, amma fa shugaban Musulmin kasar dake da zazzafar akida Shaikh Hassan Derweys ya ce fau-fau ba zai amince ba, kuma dakarunsa zasu ci gaba da gwabzawa har sai sun fatattaki dukkan sojojin ketare daga harabar Somaliya."