Afirka A jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 17.05.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka A jaridun Jamus

A wannan mako jaridun sun mayar da hankali kan halin da ake ciki a Sudan

default

´Yan gudun hijira a Darfur

Jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni da dama akan al'amuran nahiyar Afurka a wannan makon mai karewa, musamman ma a game da halin da ake ciki a kasar Sudan bayan hare-haren da ‘yan tawayen Darfur suka kai birnin Khartoum karshen makon da ya wuce. A lokacin da take gabatar da nata rahoton jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

“Nan take aka shiga farautar dubban ‘yan usulin Darfur dake zaune a birnin Khartoum, bayan da kungiyar ‘yan tawaye ta JEM ta kai farmaki, sannan kuma tayi gargadin cewar zata sake kai wani sabon harin nan gaba. Mutane kimanin 500 suka yi asarar rayukansu a yayinda wasu da dama kuma ba a ji duriyarsu ba har yanzu, lamarin da ya sanya kungiyoyin kare hakkin dan-Adam ke tababa a game da makomar wasu mutane 300 da aka ce mahukunta sun tsaresu.”

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta mayar da hankalinta ne akan martanin da fadar mulki ta Khartoum ta mayar bayan farmakin na ‘yan tawayen Darfur. Jaridar ta ce:

“Bayan farmaki na ba zata da ‘yan tawaye suka kai birnin Khartoum karshen makon da ya wuce, a nata bangaren gwamnatin Sudan ta mayar da martani na ba zata, inda ta ba da sanarwar katse dangantakar diplomasiyya tsakaninta da makobciyarta Chadi, saboda a ganinta gwamnatin Chadi na da hannu wajen shirya makarkashiyar kai wannan farmaki.” To sai dai kuma bisa ga ra'ayin jaridar ta Frankfurter Allgemeine Zeitung, wannan harin yayi kama da wanda ‘yan tawayen Chadi suka kai birnin N'Jamena farkon watan fabarairun da ya wuce. Ta la'akari da haka, ba shakka a fakaice, shugaba Idris Deby yayi murnar wannan hari da aka kai Khartoum, wanda ya zama tamkar wani mataki ne na rama wa kura aniyarta.

A halin da ake ciki yanzun hukumar zabe ta kasar Zimbabwe ta tsayar da ranar 31 ga watan yuli mai zuwa domin gudanar da zaben fid da gwani tsakanin shugaba Mugabe da abokin takararsa Morgan Tsivangirai. Jaridar Der Tagesspiegel tayi sharhi akan haka tana mai cewar:

“Ba shakka wannan wa'adi na tsawon kwanaki 90 zai ba da cikakkiyar dama ta shirya magudi a zaben. Ita kanta makobciyar kasa ta Afurka ta Kudu sai da ta nuna tababarta a game da wannan zabe a karkashin wannan yanayi na tashe-tashen hankula da ake ciki.”

Jaridar Frankfurter Rundschau tayi nuni da gurbataccen yanayin na tashe-tashen hankula da cewar:

“A wani matakin da za a iya kwatantawa da abin da Hausawa kan ce wai “Tabarmar kunya da hauka ake nade ta” shugaba Mugabe ya shiga tura dakarunsa na kundumbala domin muzanta wa jama'a bayan da yayi asarar zabe kuma martabarsa ta zube a idanun al'umar Zimbabwe. Kuma ko da yake an tsayar da ranar daya ga watan yuli mai zuwa domin zaben fid da gwani, amma ita kanta gwamnatin shugaba Mugabe ta san cewar zabe a karkashin irin wannan yanayi ba zai tafi salin-alin akan wata turba ta gaskiya ba.”

A wani mataki irin shigen na ‘yan mulkin mallaka, wanda aka fallasa a arewacin Ghana, ya sanya ala-tilas wani kamfanin kasar Norway mai samar da man fetur daga amfanin noma ya dakatar da wani shirin da ya gabatar a yankin. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

“Wani kamfanin samar da man fetur daga amfanin noma na kasar Norway ya nemi yin amfani da wani kundin dake dauke da tambarin babbar yatsar sarkin wani kauyen arewacin Ghana, wanda bai iya rubutu ko karatu ba, domin mamayar fili mai murabba'in kilomita 380 da zai yi amfani da shi wajen noma amfanin da zai iya samar da man fetur daga gare shi. Sai dai tuni aka dakatar da wannan shiri sakamakon adawa daga mazauna yankin wadanda suka ce tilas sai kamfanin ya biya tsabar kudi na dalar Amurka biyar akan wace eka daya da zai noma a filin. Tuni dai kasar ta Ghana take daukar hankalin kamfanonin samar da mai daga amfanin noma na kasashen ketare, inda kamfanonin uku na kasar Norway ke tafiyar da ayyukansu a can, a baya ga na kasashen Brazil da Sweden dake fatan yin hadin guiwa don noma da sarrafa man fetur daga rake a kasar.”

A cikin wata sabuwa kuma a farkon wannan makon ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ba da sanarwa akan tukwicin dala miliyan biyar da za a bai wa duk wanda ya taimaka aka cafke wasu mutane 13 da ake nemansu ruwa a jallo domin gurfanar da su gaban kotun kasa da kasa bisa laifin ta'asar kisan kiyashin Ruwanda a 1994. Jaridar Die Tageszeitung ce ta ba da wannan rahoto, ta kuma kara da cewar wadannan mutanen da ake nema ruwa a jallo, akasarinsu na zaune ne a kasar Kongo.