1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

November 25, 2007

Najeriya / Ghana / Tunisiya

https://p.dw.com/p/CSx9
Bagudu Hirse da SteinmeierHoto: AP

Cin hanci da rashawa na kamfanin Siemens a Najeriya

Jama´a barkanku da warhaka. To a yau zamu fara ne da tarayyar Najeriya, inda hukumar yaƙi da ci hanci da rashawa ta ƙasar wato ICPC ta fara gudanar da bincike kan zargin cin hanci da rashawa da ake zargin kamfanin sadarwa na Jamus wato Siemens da yi. A wani sharhi da ta rubuta jaridar Süddeutsche Zeitung ta fara ne da cewa batun rashawar da ake zargin kamfanin Siemens da bayarwa a Nijeriya wadda kanta take fama da matsaloli na cin hanci ya tayar da hankalin jama´a kwarai da gaske. Jaridar ta rawaito kakakin shugaba Umar ´Yar Adua na cewa an bawa dukkan hukumomi da abin ya shafa umarnin gudanar da bincike kan zargin na ba da rashawa ta euro miliyan 10 ga wasu tsofaffin ministocin sadarwa da wani jami´in shige da fice da kuma wani dan majalisar dattijai. Jaridar ta ce najeria wadda ke matsayi na biyar a tsakanin ƙasashen kungiyar OPEC waɗanda suka fi arzikin man fetir kuma ta fi kowace kasar Afirka baƙar fata fid da iskar gas, amma har yanzu kaarsa na fama da matsaloli iri daban daban sakamakon rashin iya gudanarwa da kuma masifar cin hanci da rashawa a cikin ƙasar. Ita ma jaridar Tageszeitung a rahotonta mai taken Najeriya na gudanar da bincike kan zargin cin hanci, jaridar cewa ta yi ana zargin kamfanin Siemens da raba euro miliyan 10 a matsayin hanci ga wasu masu fada a ji a harkar sadarwa mai ribar gaske a Najeriya wadda ta fi yawan al´uma a nahiyar Afirka. Ta ce wannan abin kunya ya nunar a fili yadda cin hanci ya zama ruwan dare sakamakon bude fannin harkokin sadarwa ga ´yan kasuwa masu zaman kansu a Najeriya.

Shirin EITI a kasashe masu tasowa

Yanzu kuma sai Ghana inda gwamnatin ƙasar ta yanke shawarar shiga cikin wani shiri na kula da hulɗoɗi tsakanin gwamnatoci da kamfanoni don hana cin hanci da rashawa wato EITI. A rahotonta jaridar Frankfurter Rundschau cewa ta yi wannan mataki zai ba da damar yin duba a tsarin rabon albarkatun kasa tsakanin gwamnatoci da kuma mazauna yankuna masu wannan arziki. A wani mataki don inganta halin rayuwar mazauna yankunan karkara ya sa aka kirkiro da shirin na EITI wanda ya ƙunshi kasashe masu tasowa 20 da wasu kasashe 7 dake tallafa masa. Hukumar ba da taimakon fasaha ta Jamus wato GTZ ta ke bawa kasar ta Ghana shawara don cika ka´idojin wannan shiri.

Babban taron muhalli a birnin Tunis

An yi kashedi dangane da mummunan sakamako na sauyin yanayi. Wannan dai shi ne taken rahoton da jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta kan taron nua zumunci kan sauyin yanayi da ya gudana a birnin Tunis. Jaridar ta rawaito mahalarta taron na yin kira da a gaggauta tallafawa ƙasashen Afirka da na yankin tekun Bahar Rum wadanda suka fi jin jiki sakamakon sauyin yanayi. Fiye da mahalarta taro dubu ɗaya galibi daga Afirka da Turai suka amince da wani shiri da za´a gabatarwa taron kolin MƊD kan yanayi a Bali, da zumar saukakawa Afirka ɗaukar matakan tinkarar matsalolin da ake cin karo da su sakamakon ɗumamar yanayi.

Makamashin nukiliya ga Afirka

Kungiyar EU za ta yiwa Afirka tayin tattauna huldar danganta a fannin samar da makamashin nukiliya ta hanyoyin lumana to amma ƙungiyoyin ba da taimakon raya kasa sun nuna adawa, inji jaridar Financial Times ta Jamus. Jaridar ta rawaito jami´an diplomasiya na cewa kungiyar EU za ta karfafa haɗin kai da tallafawa Afirka wajen samar da ingantaccen makamashi da hanyoyin sadarwa na zamani. To sai dai masu ba da taimakon raya kasashe masu tasowa na saka ayar tambaya ko shin wannan fasaha mai tsada, ita ce hanya mafi dacewa wajen magance matsalar karancin makashi a Afirka maimakon a mayar da hankali wajen inganta hanyoyin samar da makamashi ta iska ko hasken rana.