1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

November 21, 2007

Somalia / Yankin Ƙahon Afirka / Sudan

https://p.dw.com/p/CIQJ
Yara Matasa da BindigogiHoto: AP

Rikicin kasar Somalia

A wannan makon dai halin da ake ciki a ƙasar Somalia ya fi ɗaukar hankalin jaridun na Jamus. A sharhin da ta rubuta jaridar Frankfurter Rundschau cewa ta yi dubun dubatan ´yan Somalia na tserewa daga ƙazamin faɗa yayin da MƊD ta yi kashedi kan aukuwar wani bala´i dake zaman matsala mafi muni da ɗan Adam ke fuskanta a nahiyar Afirka ciki har da halin da ake ciki a lardin Darfur na yammacin ƙasar Sudan. Jaridar ta rawaito wakilin MƊD a ƙasar Ahmadu Ould-Abdallah na cewa halin da ake ciki yanzu a Somalia ya fi na ko-ina a nahiyar Afirka yin muni. Yanzu haka dai babu mai iya tabbatar da tsaron lafiyar mutane dubu 170 da suka tsere daga Mogadishu da ma waɗanda suka saura a birnin. Sannan hukumar kula da ´yan gudun hijira ta MƊD ta ce yanzu ta fara rarraba kashi na ƙarshe na kayan abinci da suka saura a rumbunta dake babban birnin na Somalia.

Rashin sanin tabbas a yankin ƙahon Afirka

A rahoton da ta rubuta kan rikicin na Somalia jaridar Tageszeitung cewa ta yi yankin Kahon Afirka ya shiga cikin wani hali na tsaka mai wuya. Ta ce a Somalia faɗa na ƙara yin muni sannan wani yaki na barazanar ɓarkewa tsakanin Ethiopia da Eritrea, yayin da Sudan kuma ke cikin halin rashin sanin tabbas kan siyasar ƙasar. Ta ce a tsakiyar waɗannan rikice rikicen kuwa akwai sojojin ƙasa da ƙasa masu kayan aiki na zamani to sai dai ba sa iya taɓuka komai don dakatar da wannan ruɗani. Jaridar ta kara da cewa yanzu dai hankalin gamaiyar kasa da kasa ya fi karkata zuwa Sudan, inda a nan ma rikicin yake son ya gagari kundila. Yanzu haka dai makomar yankin na Kahon Afirka ya fi a kowane lokaci shiga mawuyacin hali, to amma babu wata manufa ta a zo a gani da gamaiyar ƙasa da ƙasa ke da ita don gano hanyoyin magance matsalolin.

Shirin tura dakaru a Darfur ka iya ci-tura

A wani rahoto mai taken shirin MƊD na girke dakaru a lardin Darfur na barazanar rugujewa jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi tsokaci tana mai cewa babu isasssun kayan aiki ciki har da jiragen sama masu saukar ungulu ga wannan runduna. Jaridar ta ce rundunar na bukatar jiragen sama masu saukar ungulu aƙalla guda 24 ciki har da yaki guda shida da na jigilar kaya 18, don wannan aiki yayi nasara. To amma kawo yanzu babu wata ƙasa da ta nuna shirin ba da wadannan jiragen sama. To sai dai a wani abin da ke zama mai son zuwa sama idan ya taka takarda ya rage hanya, a ranar alhamis majalisar dokokin Jamus ta kada kuri´ar amincewa da aike sojojin sa ido 75 zuwa kudancin Sudan da na rundunar Bundeswehr 250 zuwa lardin Darfur. Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi sharhi kan hali da ake ciki a Darfur tana mai cewa gwamnatin Khartoum ta sawa sansanonin ´yan gudun hijira ido. Ta ce tun bayan ake samun rahotanni dangane da yawaitar makamai da wuraren horas da sojoji a sansanonin ´yan gudun hijira a Darfur. Ta ce da yawa daga cikinsu magoya bayan kungiyar ´yan tawaye ta Sudan Liberation Army ne. Waɗannan sansanonin dai musamman waɗanda ke kusa da manyan birane suna zamewa gwamnati tamkar kadangaren bakin tulu.

Ziyarar Köhler a arewacin Afirka

Shugaban Jamus Horst Köhler ya yaba da sauye sauyen da ake aitwarwa a Aljeriya. Taken rahoton da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta kenan game da ziyarar wadda take zaman ta farko da wani shugaban Jamus ya kai ƙasar ta Aljeriya. Jaridar ta ce duk da gamsuwar da Köhler ya nuna dangane da kokarin da gwamnatin shugaba Bouteflika ke yi wajen aiwatar da canje canjen, a lokaci daya kuma shugaban na Jamus ya yi tsokaci dangane da matsalolin da har yanzu Aljeriya ta kasa magance su. Bayan shekaru masu yawa tana fama da rikici da ´yan ta´adda na musulmi da matakan ba sani ba sabo da sojoji ke ɗauka kan ´yan takife yanzu dai kasar ta na kan turbar yin sulhu. Shugaban na Jamus ya kuma ziyarci kasar Mauritaniya.