1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

November 14, 2007

Tschadi / Kenia / Kongo / Ghana

https://p.dw.com/p/C85a
Shugaban Faransa SarkozyHoto: picture-alliance/dpa

Rikicin sace yara a Tchadi

To a yau zamu fara ne da wani rahoto da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta wanda a ciki ta rawaito shugaban Faransa Nicolas Sarkozy na cewa zai taho da sauran turawan da aka tsare da su a Chadi gida. Jaridar ta ce bayan da shugaba Sarkozy ya shawo kan shugaban Chadi Idris Deby ya saki ´yan jaridar Faransa 3 da ma´aikatan jirgin sama ´yan Spain su 4, shugaban na Faransa ya lashi takobin samun sakin sauran turawan ba tare da la´akari da laifin da suka aikata ba. Su dai turawan 10, 6 daga cikinsu ma´aikatan kungiyar agajin nan ta L´Arche de Zoe ana shirin gurfanad da su gaban kuliya a kasar Chadi bisa yunkurin sace yara da kuma yin zamba ciki aminci. Jaridar ta kuma rawaito wata jaridar Faransa wadda ta ambato ministan cikin gidan Chadi Ahmat Mahamat Bachir yana mai bayyana turawan da barayi. Ministan ya ce za´a yi musu shari´a ta gaskiya a Chadi kuma duk wani yunkurin mayar da su Faransa zai zama tamkar cin fuska ga Afirka. Ya ce in an same su da laifi to dole ne su yi kurkuku a Chadi.

Tallafi daga kasashen turai

A wani rahoto na daban jaridar ta Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rawaito wani jami´in gwamnatin Kenya na zargin wata kungiyar agaji ta kasar Amirka da cinikin bayi da kuma ci da gumin kananan yara. Jaridar ta rawaito wani lauya a Kenya na cewa an yi karar reshen kungiyar da ake kira Kids Alive International a dangane bacewar wasu yara 3 dake karkashin kulawar sa. Kuma ta a ranar 9 ga watan oktoba aka haramta ayyukan kungiyar a Kenya.

Rikici a Kongo

A rahoton da ta rubuta mai taken an soki lamirin masu zuba jari a Kongo, jaridar TAZ ta ce sakamakon wani bincike da kwamitin kula da kwagiloli a JDK ya yi, ya ba da shawarar soke dukkan kwangiloli na aikin hakan ma´adanai. Yanzu haka dai aikin hakan ma´adanai a Kongo na fuskantar barazanar rugujewa. A lokacin yakin kasar cikin shekaru 10 da suka wuce kamfanoni sun yi ta rige-rigen sayen hannayen jari da rahusa, a hanyoyin da suka sabawa dokokin kasa. A saboda haka a cikin watan afrilu sabuwar gwamnatin Kongo ta kafa wani kwamiti don gudanar da bincike kan kwangilolin. Kwamitin ya gano cewa kamfanonin musamman na ketare sun bi barauniyar hanya kana kuma ba sa cika ka´idojin yarjeniyoyin kwantaragi da gwamnati. Hakan na jawowa kasar babbar asara ta kudaden shiga. Yanzu kuma sai nan Bonn inda a farkon mako gwamnatin jihar NRW da kasar Ghana suka yi bukin sanya rattba hannu kan yarjejeniyar bawa juna hadi kai. A sharhin da ta rubuta jaridar GA ta jaddada muhimmancin irin wannan hadin kai a fannin aikin raya kasashe. Ta ce samun bunkasar jama´a da habakar tattalin arziki a Afirka ya samar da kyakkyawan yanayi inganta huldodi da kasashen nahiyar. To sai dai matsala dai har yanzu shine kasashen sun fi samun kudaden shiga ne daga danyun kayan da suke sayarwa ketare wanda a lokutan baya ya janyo cin hanci da rashawa ba tare da an samu ci-gaba ba.

Jamus ta bawa Ghana taimako

Ita ma jaridar Frankfurter Rundschau ta yi tsokaci akan yarjejeniyar hadin kan tsakani Ghana da jihar NRW. Jaridar ta rawaito ministan harkokin wajen Ghana Akwasi Osei Adjei na cewa a tattaunawar da suke yi kan harkokin ciniki da KTT, kasashen Afirka ba zasu yarda su yi watsi da karbar kudaden kwastan ba. To sai dai tambaya a nan ita ce shin kawunan kasashe sun hadu? Dole ne kasashen KTA su samun matsaya daya. To amma ko wace kasa tana shiga cikin tattaunawar ne a matsayin ´yantacciyyar kasa kuma tana kokarin kare bukatunta ne kawai. Yanzu kuma sai kasar Kenya inda kungiyoyin kare hakin ´yan Adam ke zargin ´yan sanda da yiwa daruruwan mutane kisan gilla a yakin da ake yi da masu aikata laifuka. A rahoton da ta rubuta jaridar TAZ ta ce tun a cikin watan yuni an yi rajistar gawawwaki 454 wadanda aka harbe su a ka. Kusan dukkan su kuwa matasa ne ´yan kabilar Kikuyu, wadanda gwamnati a Nairobi ta ce masu aikata laifuka ne wadanda ke addabar jama´a.