Afirka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 05.11.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka A Jaridun Jamus

Ana zargin kungiyar da yunkurin sace yara daga Chadi zuwa Faransa.

Wasu ma´aikatan kungiyar

Wasu ma´aikatan kungiyar

Jama´a barkanku da warhaka. To a wannan makon jaridun sun fi mayar da hankali ne akan yunkurin da wasu turawan Faransa suka yi na sace wasu yara daga Chadi zuwa kasar ta Faransa. A wani sharhi da ta rubuta jaridar SdZ ta fara da cewa kungiyar agaji ta Arche de Zoe ba zata iya wanke kanta daga zargin yin garkuwa da kananan yara ba. Ta ce akwai tambayoyi da dama amma har yanzu ba´a ba da wata amsa mai gamsarwa ba. Shaidar da kungiyar ta ce tana da ita cewar yaran marayu ne daga yankin Darfur kuma shugabannin kauyuka na wannan lardi suka amince da fid da su, ba kwakkwara ba ce. Domin duk wasu takardun shaida musamman daga yankin da ake fama da rikici kusan a ce ba ta da wata daraja tun da ba wanda ke iya tabbatar da sahihancinsu. Sannan da yawa daga cikin yaran sun ce iyayen su na nan da rai kana kuma babu daya daga cikin su da ya nuna wata alama ta tagaiyara. Hakazalika jirgin saman da aka yi catarsa an yi masa rajistar jirgin daukar marasa lafiya ne, wato kenan turawan sun gabatar da takardun boge ne domin sace yaran daga Afirka. Ita ma a sharhin ta jaridar Neues Deutschland ta fara ne da cewa yunkurin sace yara daga Chadi ya haddasa wani abin kunya na siyasa a Faransa. Yayi da shugaban idris Deby ya kwatanta wannan abu da cinikin bayi, shi kuwa shugaban ´yan adawa na Chadi Yorongar Ngarley cewa ya fusata yana mai cewa yayin da Faransa ta kafa sabuwar dokar shigan baki kasar musamman ga yara da iyayensu ke zaune a Faransa sai ga shi wata kungiyar agaji zata yu sumogar yara 103 zuwa Faransa ba tare da wata takardar shaida ba. A na rahotonta jaridar FAZ ta rawaito shugaban Faransa Nicolas Sarkozy na sukar kungiyar agajin da cewa abin ta yi a Chadi haramun ne kuma rashin sanin mutunci kai ne. Jaridar ta nuna damuwa cewar wannan abin kunya na yunkurin cinikin kananan yara ya sa ana saka ayar tambaya danagne da shirin KTT na girke dakarun zaman lafiya a kasar Chadi. Ita kuwa a rahonta jaridar TAZ ta rawaito wani ma´aikacin kungiyar agaji ta CARE Thomas Schwarz yana cewa ko da yake ana iya kwatanta abin da kungiyar ta Arche de Zoe ta yi da cewa tausayawa ne ga yaran, amma ta tabka tabka babban kuskure. Kwashe yaran daga yankin da ake fama da yakin zuwa wani bakon wuri cikin wata bakuwar al´ada zai kara jefa su cikin mawuyacin hali ne. Ya ce duk mai sha´awar taimakawa yara a Darfur ko a Chadi to dole ya taimaka musu a cikin kasar, inda yayi nuni da aikace aikace da ake yi a Ruanda inda aka bari ´yan kasar da kansu ke kula da marayu.

Yanzu kuma sai Libya inda aka gudanar da taron sulhu tsakanin gwamnatin Sudan da ´yan tawayen Darfur. A sharhin da ta rubuta jaridar FAZ ta ce kauracewa taron da manyan kungiyoyin ´yan tawaye suka yi ya sa wannan taro bai samar da wani abin kirki kamar yadda aka yi fata ba. Haka kuwa na zaman wani karar tsaye ga samun nasarar rundunar hadin guiwa da tsakanin KTA da MDD da ake shirin turawa a yankin.

´Yan kasar Kongo na kare kansu daga yaki. Wannan dai shi ne taken wani rahoto da jaridar TAZ ta rubuta a dangane da rikicin gabashin JDK. Jaridar ta ce yanzu ana kara samun masu adawa da kuma aikace aikacen kare kai daga rikicin gabashin Kongo da kuma karuwar masu aikata laifu ka a yankin. Ta ce mazauna yankin sun fid da kaunar cewa gwamnati zata iya samar da tsaro a yankin. Saboda gazawar gwamnati na kare al´uma dalibai da matasa a garuruwa kamar Butembo da Goma da sauran yankuna na arewacin lardin Kivu suna kakkafa kungiyoyin yaki da miyagu da sauran masu aikata laifi.

 • Kwanan wata 05.11.2007
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/C1cI
 • Kwanan wata 05.11.2007
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/C1cI