Afirka A Jaridun Jamus 130204 | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 13.02.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka A Jaridun Jamus 130204

Masu sauraro barkanku da warhaka. To a yau zamu fara ne akasar Sudan, inda gwamnatin wannan kasa ta ba da sanarwar samun nasara akan ´yan tawayen yankin Dafur. A cikin wani rahoto da ta rubuta, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rawaito shugaban Sudan Hassan al Bashir na fadi a cikin wata sanarwa da ya bayar cewar ya samu nasara akan ´yan tawayen Jihar Dafur dake yammacin wannan kasa. A dangane da haka shugaban yayi shailar kawo karshen matakan soji da yake dauka a wannan yanki. Ko da yake kakakin daya daga cikin kungiyoyin ´yan tawaye 3 na wannan yanki ya karyata ikirarin na shugaba al-Bashir, amma ya tabbatar da cewa dakarun gwamnati sun fatattaki na ´yan tawaye daga kusan dukkan garuruwa na wannan jiha. A lokaci daya kuma shugaba Al Bashir ya yiwa mayakan kungiyoyin ´yan tawayen afuwa, muddin sun ajiye makamansu a cikin makonni 4 masu zuwa. Wannan sanarwar ta zo ne kwanaki kalilan gabanin wani taro da ake shirin yi tsakanin bangarorin dake rikici da juna a birnin Geneva, to amma gwamnatin birnin Khartoum ba ta sha´awar halarta. Jaridar ta ce ko da yake gwamnatin Sudan na tattauna batun samar da zaman lafiya da ´yan tawayen kudancin kasar, amma ta ki ta yi hakan da al´umar yankin Dafur, wadanda daukacinsu bakaken fatu ne. Haka zalika jaridar ta yi zargin cewa kasar Amirka wadda ke taka muhimmiyar rawa a tattaunawar samar da zaman lafiya tsakanin kungiyar SPLA da gwamnatin Sudan, har yanzu ba ta fito fili ta nuna matsayinta game da ta´asar da dakarun gwamnati ke yi a Dafur ba. Batun samar da zaman lafiya a Sudan din dai ne abin da ya fi daukar hankalin jaridar Tageszeitung. Jaridar ta ce bayan an shafe shekara daya da rabi ana gudanar da shawarwari tare da kulla wasu yarjejeniyoyi, yanzu aski ya kai gaban goshi game da cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnati a birnin Khartoum da kuma ´yan tawaye a kudancin Sudan. Jaridar ta yi fatan cewa komawa da za´a yi kan teburin shawarwari a ran talata mai zuwa, zata kai ga cimma tudun dafawa, don samun damar mayar da dubun dubatan ´yan gudun hijirar kudancin Sudan yankunan su na asali.

Ita kuwa jaridar Frankfurter Rundschau ta tabo batun kasar Liberia ne, wadda aka yiwa alkawarin ba ta taimako na dala miliyan 520 don sake gina wannan kasa bayan ta shafe shekaru 14 tana fama da yakin basasa. An dai tara wadannan kudade ne a gun wani taron kasashen da ke ba da tallafi da ya gudana a hedkwatar MDD dake birnin New York. Jaridar ta ce ko da yake wannan taron ya ba da damar dinke barakar da ta taso bara tsakanin sakataren harkokin wajen Amirka Colin Powell da takwaransa na Faransa de Villepin dangane da Iraqi, amma duk haka da sauran rina a kaba, domin Powell ya ce Amirka ba zata ba da gudummawar dakaru a rundunar kiyaye zaman lafiya da Faransa ta yi kira ga MDD ta girke a kasar Ivory Coast. A game da Liberia kuwa MDD ta amince ta girke dakaru kimanin dubu 15. Yanzu kuma sai kasar ATK inda jaridar TAZ ta rawaito cewar shugaban kasa Thabo Mbeki ya tsayar da ranar 14 ga watan afrilu ta zama ranar da za´a gudanar da babban zaben kasar, to amma har yanzu rabin masu zabe ne suka yi rajista a wannan kasa. Za´a gudanar da zaben ne kuwa a daidai lokacin da ake bikin cika shekaru 10 da kawo karshen mulkin nuna wariyar fata a wannan kasa, to amma har yanzu halin rayuwar da yawa daga cikin bakaken fatun wannan kasa bai canza ba, inji jaridar ta TAZ. Hakan dai wani babban kalubale ga gwamnatin shugaba Mbeki, amma maimakon gwamnati ta canza alkibla bisa manufar magance matsalolin talauci da fatara da cututtuka kamar AIDS da suka yiwa bakar fata katutu, har yanzu ba ta nuna wata alamar yin haka din ba. A game da kasar JDK ma har wayau jaridar ta TAZ ta labarto mana shirye-shiryen da ake yi na gudanar da zabe a wannan kasa a cikin shekara mai zuwa. Jaridar ta ce Kongo ce wata kasa a nahiyar Afirka da al´umar ta ba su taba jefa kuri´a ba, to amma hakan zai canza, lokacin da al´umar wannan kasa zasu zabi wata sabuwar gwamnati a shekara ta 2005.

Wannan gwamnati dai ita zata maye gurbin gwamnatin rikon kwarya da aka kafa a bara, wadda ta kunshi dukkan bangarorin dake gaba da juna a kasar ta Kongo.
 • Kwanan wata 13.02.2004
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvqA
 • Kwanan wata 13.02.2004
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvqA