1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afghanistan ta kori wasu Jami'an EU da na Majalisar Ɗinkin Duniya

December 27, 2007
https://p.dw.com/p/Cgfc

Majalisar Ɗinkin Duniya da Ƙungiyar Taraiyar Turai sun sanar da cewa jami’ansu biyu da aka kora daga ƙasar Afghansitan sun taso daga birnin Kabul yau Alhamis kan hanyarsu ta komawa gida. Gwamnatin Afghanistan tana zargin jami’an biyu, ɗaya ɗan kasar Burtaniya da ɗan Ireland da laifin yin zagon ƙasa ga harkokin tsaron ƙasar. Gwamnatin tace jami’an sun gana ne da wasu ‘yan Taliban ba tare da neman izni ba saboda haka ta basu sa’o’i 48 daga ranar Talata da su fice daga ƙasar.Majalisar Ɗinkin Duniya dai tace rashin fahimta ne ya haddasa wannan batu,tana mai baiyana cewa jami’an biyu sun kai ziyara ne garin Musa Qala inda yan Taliban suke riƙe da shi na tsawon watanni 10 kafin wani ɗauki da aka kai makonni biyu da suka shige. Jamian Ƙungiyar Taraiyar Turai sunce ana tattauna batun tsakanin manyan jami’an ɓangarorin biyu da suka haɗa da kantoman kula da harkokin wajen ƙungiyar, Javier Solana.