Afghanistan bayan zaɓe | Siyasa | DW | 21.08.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Afghanistan bayan zaɓe

Hukumar zaɓen ƙasar Afghanistan ta ce ta kammala ƙidayar ƙuri´u biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa da na ƙananan hukumomi da ya gudana a jiya Alhamis.

default

Shugaban Afghanistan Hamid Karzai

Alƙalumman da hukumar ta bayar sun yi nuni da cewa kimanin kashi 50 cikin 100 na waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri´a suka sauke wannan farali. Yanzu haka dai ana sasa ran samun sakamakon zaɓen a cikin mako mai zuwa.

Ko da yake har yanzu demukuraɗiyya jaririya ce a Afghanistan amma babu tantama game da imanin da ɗaukacin mazauna Kabul babban birnin ƙasar suka yi ga wannan tsari kamar yadda wannan matashin ya nunar.

Ya ce: "Bawa mutane damar kaɗa ƙuri´a za su iya zaɓan gwamnati mafi dacewa a garesu kuma Afghanistan ka iya shiga jerin ƙasashe mafiya kyau a duniya."

Ga wannan matashin kaɗa ƙuri´ar na zaman wani farali ne na ƙasa da kuma musulunci. Ko shakka babu da yawa daga cikin ´yan ƙasar na fatan cewa ƙuri´unsu ba za su tafi a banza ba sannan a ƙarshe demokuraɗiyya za ta yi nasara a Afghanistan. Ga shugaba Hamid Karzai tuni ya haƙiƙance akan haka.

Ya ce: "Mutanen Afghanistan ba su ji tsoron bama-bamai da rokoki ko wata tursasawa ba. Sun fita ƙwansu da kwarkwatansu don kaɗa ƙuri´a. Mu dai ga yadda aka yi zaɓe wannan gagarumin abu ne."

Kaɗa ƙuri´a a cikin wani hali dake da barazana ga rayuka ya kasance tabbas ga ɗaukacin ´yan Afghanistan. A jimilce mutane 50 rabi daga ciki ´yan tawaye suka rasa rayukansu sakamakon hare hare da aka kai jiya a faɗin ƙasar baki ɗaya. Hatta a yankin arewacin ƙasar inda aka girke sojojin Jamus ma an kai harin rokoki, sannan ´yan sanda sun sanar da cewa an halaka ´yan tawaye fiye da 20 a wata musayar wuta da aka yi a garin Baghlan. Tsauraran matakan tsaro da aka ɗauka a birnin Kabul ya katse hanzarin ´yan ta da zaune tsaye inji shugaban hukumar leƙen asiri Afghanistan Amarullah Sale.

Ya ce: "Babu wani tashin hankali na a zo a gani da ya faru. ´Yan sanda biyu sun samu raunuka lokacin da suka yi ƙoƙarin katse hanzarin maharan ƙunar baƙin wake shida. Ba a taɓa samun haka ba. Wannan abin alfahari ne wanda ya bawa duniya baki ɗaya mamaki."

To sai dai duk da waɗannan kalaman yabo daga bakin shugaban hukumar leƙen asirin, tambayar da da yawa daga cikin masu sa ido a zaɓe suka yi ita ce ko barazanar kai hare hare da Taliban ta yi kwanaki ƙalilan gabanin zaɓen ta ƙara tsorata mutane har suka ji tsoron barin gidajensu. To sai dai ga wannan talikin da bai zaɓe ba hakan bai taka wata rawa ba.

Ya ce: "Wannan zaɓen ya na da kyau ga masu arziki da kuma manyan ´yan kasuwa. A garemu talakawa kam babu wani abin da zai canza a rayuwarmu."

Masu sa ido a zaɓe sun ce haƙiƙa a zaɓen ya gudana a shekara ta 2004 su ga dogayen layuka fiye da na jiya musamman a birnin Kabul da sauran lardunan ƙasar ta Afghanistan.

Mawallafa: Kai Küstner/Mohammad Awal

Edita: Yahouza Madobi