Afghanistan: Bam ya tashi a sansanin sojan sama na NATO | Labarai | DW | 12.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Afghanistan: Bam ya tashi a sansanin sojan sama na NATO

Mutane akalla hudu sun mutu yayin da wasu 14 suka jikkata, bayan da wani abu mai kama da bam ya tarwatse a sansanin sojojin sama na kungiyar NATO da ke Bagram mai nisan kilomita 50 a arewacin birnin Kabul.

Fashewar abun dai ta wakana ne da asubahin wannan Asabar din kusa da wani dakin cin abinci. Sai dai kuma ba a san dalilin da ya haddasa hakan ba. A cewar wata majiya ta dakarun na NATO a kasar ta Afghanistan, fashewar wannan abu ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, kuma tuni ma'aikatan agaji masu yawan gaske suka nufi wurin domin bada agajin gaggawa.

A daran Alhamis wayewar Juma'a ma dai, an kai wani hari a karamin ofishin jakadancin kasar Jamus da ke Mazar-i-Sharif mai nisan kilomita 380 a arewa maso yammacin birnin na Bagram, harin da 'yan Taliban suka dauki alhakin kai shi wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutane shida sannan wasu 120 suka samu raunuka. Wannan sansanin sojojin na NATO da ke a Bagram dai na kunshe  da sojoji akalla 9,800 na kasar Amirka da har yanzu suke kasar ta Afghanistan.