Addu´o´i ga wadanda suka rasu a rushewar rufin wani gini a Jamus | Labarai | DW | 07.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Addu´o´i ga wadanda suka rasu a rushewar rufin wani gini a Jamus

Kwanaki 5 bayan hadarin rushewar rufin wani ginin wasan kankara a garin Bad Reichenhall dake kudancin Jamus, a yau sama da mutane dubu daya da 500 sun halarci addu´o´in da aka yiwa mutane 15 da suka rasu sakamakon wannan hadari. Bayan ga ´yan´uwa da abokannen wadanda hadarin ya rutsa da su, ma´aikatan ceto su ma sun halarci wajen addu´o´in. An dai hana ´yan jaridu da masu daukar hoto shiga cikin cocin Saint Zeno, inda aka gudanar da addu´o´in. Shugaban tarayyar Jamus Horst Köhler wanda ya dan makara zuwa wajen addu´o´in ya sanya sunansa a rajistar masu ta´aziya. A ranar talata mai zuwa za´a yi jana´izar a hukumance.