1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adduo'i ga sojin Jamus da suka rasu a Mali

July 30, 2017

Ministar tsaro a Jamus Ursula von der Leyen ta hallaci taron addu'oi ga sojojin kasar biyu da suka mutu a hadarin jirgin sama a kasar Mali. 

https://p.dw.com/p/2hPbw
Von der Leyen reist nach Mali und Niger
Hoto: picture alliance / Britta Pedersen/dpa

A yayin taron addu'oin Ministar ta bayyana alhininta kan wannan babban rashi. Sojin Jamus akalla dari daya ne suka halaci taron adduo'in a sansanin sojin kasar da ke birnin Gao a arewacin Mali, Ursula von der Leyen ta jadadda matakin gwamnatin Jamus na tabbatar da zaman lafiya a kasashen Afrika wanda ta ce shi ne ginshikin zaman lafiya a kasashen Turai.
 
Sojojin na daga cikin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali wato MINUSMA, suna aikin gudanar da aikin binciken sirri a lokacin hadarin da ya yi sanadiyar rayukansu a ranar Larabar da ta gabata. Kawo yanzu dai ba a tantance musababbin aukuwar hadarin ba.


Ana sa ran Ministar tsaron kasar ta Jamus za ta kai ziyara aiki a Jamhurriyyar Nijar nan gaba.