1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adawar Nijar ta kaurace wa zaman majalisa

Mouhamadou Awal BalarabeMarch 24, 2016

Daukacin 'yan majalisa da aka zaba karkashin jam'iyyun adawar Nijar sun ki halartar bikin girka sabuwar majalisar dokoki da ya gudana a babban birnin kasar wato Yamai.

https://p.dw.com/p/1IJQ0
Sitzung des Parlaments in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

'Yan adawa a Jamhuriyar Nijar sun kaurace wa bikin girka sabuwar majalisar dokoki, kwanaki 33 bayan zaben 'yan majalisa da ya gudana a ranar 21 ga watan Fabrairun 2016. Babu ko da dan majalisa daya daga cikin 53 na bangaren adawa da ya halarci babban zauren taro na Palais des Congres na birnin Yamai inda aka yi wannan zama.

Zababbun 'yan majalisa uku na bangaren adawa ne ke gidan yari yanzu haka, bisa zarginsu da ake yi da mara hannu a yunkurin juyin mulkin watan Disamban 2015 da ya ci tura.

Gamayyar jam'iyyun adawa ta COPA ta ki amincewa da sakamakon zabe zagayen farko da na biyu da suka gudana. Sai dai bangaren shugaba Mahamadou Issoufou da masu goyon bayansa na da cikakken rinjaye a wannan majalisa, inda kawancen da ke mulki ke da 'yan majalisa 118 daga 171 da majalisar ta kunsa.

Shugaba Mahamadou Issoufou ya yi kira ga 'yan adawa da su amince da shiga cikin gwamnatin hadin kan kasa da yake niyar kafawa. Sai dai har yanzu ba su ce uffan ba game da wannan tayin da aka yi musu.