Adawa ta ƙwaci mulki a Kirgistan | Labarai | DW | 08.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Adawa ta ƙwaci mulki a Kirgistan

Madugun ´yan adawar Kirgistan Roza Otunbayewa ya naɗa kansa a matsayin saban Firaministan riƙwan ƙwarya

default

Zangar-zangar ´yan adawa a Kirgistan

`Yan adawa a ƙasar Kirgistan, sun  tabbatar da ƙwatar mulki a sakamakon zanga-zangar gama gari da magoyan bayansu suka shirya jiya, domin ƙalubalantar shugaba Kurmanbek Bakiyev.

Madugun ´yan adawar Kirgistan Roza Otunbayewa ya aiyyanar da kansa a matsayin saban Firaminista riƙwan ƙwarya na wannan ƙasa dake tsakiyar Asiya, wadda kuma ke fama da yawan rikicin siyasa.

Rahotanin sun nunar da cewar, shugaba Bakiyev ya tsere daga babban birnin Bishkek, zuwa Osh dake kudancin ƙasar.

Masu zanga-zangar sun bayyana zarge-zargen da suke wa shugaban ƙasa:

"Shugaban ba abin da ya sa gaba illa yin rabda ciki da dukiyar jama´a, da kuma cin hanci da rashawa, tare da take haƙƙoƙin bani adama, sannan rayuwa tayi matukar tsada a Kirgustan."

Ya zuwa yanzu, mutune aƙalla 65 suka rasa rayuka  a cikin wannan zanga-zanga.

Ƙasashen Rasha da Amurika wanda keda rundunonin soja a Kirgistan, sun yi kira ga jama´a su kwantar da hankali.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Umaru Aliyu