Adawa da zaman sojojin NATO a Afganistan | Labarai | DW | 30.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Adawa da zaman sojojin NATO a Afganistan

Mutuwar mutane huɗu ta haifar da kiran janye dakarun NATO a Afganista

default

Sojojin NATO a Afganistan

Wasu ɗaruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Amirka dake Kabul, domin nuna fushin su ga halaka wasu fararen hula huɗu a wani hatsarin mota da ya rutsa da motocin dakarun yaƙin  NATO.

Hotunan talabijin a ƙasar ta Afganistan sun nuna motocin Sojin na NATO na cin wuta bayan da wasu matasa suka huce haushin su akan su, tare da suka ga shugaba Hamid karzai da kuma kira a janye sojojin AMirka da ƙawayen ta daga Afganistan.

Kanfanin dillancin labaran AP yace saida 'yansanda suka harba bindiga domin tarwatsa masu zanga-zanga da ke jifa da duwatsu tare kuma da ƙona wata motar Sojojin tsaron ƙirar SUV a wannan hatsari daya auku akan hanyar zuwa filin jirgin sama na birnin Kabul.

Makamancin wannan hatsari ya haifar da mummunar zanga-zanga ƙin jinin Amirka da ƙawayen ta a shekara ta 2006 a lokacin da mutane 14 suka rasu.

Mawallafi:Babangida Jibril

Edita:Umaru Aliyu