1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adawa da zaben raba gardamar côte d'Ivoire

October 28, 2016

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun tarwatsa zanga-zangar da aka shirya a Abidjan da nufin nuna adawa da zaben raba gardama na Côte d 'ivoire.

https://p.dw.com/p/2RrA7
Elfenbeinküste Referendum Wahl Abidjan
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga a birnin Abdijan na Côte d' Ivoire don nuna adawa ga zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki da zai gudana a ranar mai zuwa Lahadi idan Allah ya yarda. Sai dai jami'an kwantar da tarzoma sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa gungun masu zanga-zanga da suka zarta wuraren da aka kayyade musu.

Gamayyar jam'iyyun adawa da ake yi wa lakabi da "Front du refus" ne ta bukaci da a gudanar da wannan zanga-zanga domin yin tir da abin da ta kira share fagen dawwama a mulki da shugaba Alassane Ouattara ke yi. Dama dai ta yi kira ga magoya banta da suka kaurace wa wannan zaben raba gardama.

Daftarin sabon kundin tsarin mulkin ya tanadi mukamin mataimakin shugaban kasa da kuma kafa majalisar dattawa, tare da tantance hanyoyin zama dan kasa. Tun a yakin neman wa'adi na biyu na mulki ne, Ouattara ya yi alkawarin samar da sabon kundin tsarin mulki da zai sa a juya babin rikicin siyasa da aka shafe shekaru 10 ana fama da shi a Côte d' Ivoire.