Adawa da yaƙin Irak ta gama dunia | Labarai | DW | 19.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Adawa da yaƙin Irak ta gama dunia

ƙasashe daban daban a nahiyar turai, sun shirya tafiyar jerin gwano, cikin limana a ranar jiya assabar, domin yin Allah wadai, ga yaƙin ƙasar Iraƙi.

A Britania,, a na kyauttata zaton, mutane kussan dubu 100 ne, su ka hito cikin titina, domin kira ga gwamnatin Tony Blair, ta janye sojojin ta, daga Iraƙi.

Kazalika a ƙasashen Italia , Danmark, Girka,Holland, da sauran su, inda rahotani su ka bayyana cewar, dubun dubunan mutane, sun yi cincinrido, bisa titina, don ƙalubalantar wannan yaƙi, da su ka dangata da haramce.

An gudanar da wannan zanga zanga a turtai da Amurika, albarkacin cikwan shekaru 3, da Amurika, tare da sojojin ƙawance, su ka kiffar da Saddam Hussain, su ka kuma kaka gida a Iraki.

A halin yanzu ƙasashen Amurika, Britania, da Italia ,ke da sojoji mafi yawa, a wannan ƙasa.