1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adawa da tsuke bakin aljihu a Turai

September 29, 2010

Dubban masu adawa da tsarin tsuke bakin aljihun da gwamnatoci a ƙasashen EU, suka shiga zanga-zanga a yau

https://p.dw.com/p/PPtU
Dubban masu zang-zanga a BrusselHoto: AP

A ƙasar Spain yajin aiki na sa'o'i 24 ya kawo cikas ga harkar sufuri da sauran ma'aikatun ƙasar. Wannan yajin aiki zai shafi dubban masu yawon buɗe ido, kasancewa an soke tashin jiragen sama, kama da cikin Turai da sauran sassan duniya. Ƙungiyoyin ƙwadugo na yajin aikin ne, don nuna adawarsu da shirin tsuke bakin aljihu da garanbawul ɗin da gwamnatin ƙasar ta shiryawa fannin kasuwanci. An bada rohotonni raunata mutane aƙalla 20 sakamakon zanga zangar. 'Yan ƙwadugo dai sukace an samu nasara, kamar yadda wannan take cewa. "Muna farin ciki da yadda ma'aikata suka amsa shiga yajin aikin, ina ganin komai ya tsaya cik a babban birnin ƙasar wato Madrid a sakamakon yajin aikin".

A halin da ake ciki kuwa dubban masu zanga-zanga ne suka hallara a a birnin Brussel, inda suke nuna adawa da shirin tsuke bakin alhihu da gwamnatoci masu amfani da kuɗin euro suka ɗauka, a wani tsarin da ƙasashen ke yi, don ceto darajar kuɗin na euro. Ƙungiyoyin ƙwadugo daga Turai sukace suna saran hallartar mutane kimanin dubu takwas cikin zanga-zangar ta Burasel.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu