ADAWA DA DAKARUN MAMAYE A IRAQI NA TA KARA TSAMARI | Siyasa | DW | 08.04.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ADAWA DA DAKARUN MAMAYE A IRAQI NA TA KARA TSAMARI

A kasar Iraqi, rikici sai kara muni yake yi. Ana ta ci gaba da fafatawa tsakanin sojojin mamayen ketare da Amirka ke yi wa jagoranci, da `yan adawan kasar.

Hayakin bam, da dakarun Amirka suka jefa kan wasu gine-gine, a garin Falluja

Hayakin bam, da dakarun Amirka suka jefa kan wasu gine-gine, a garin Falluja

Shekara daya, bayan afka wa Iraqi da yaki da kuma hambarad da gwamnatin Saddam Hussein da Amirka ta yi, ba a sami sassaucin tsamari a kasar ba har ila yau. Wasu masharhanta ma na ganin cewa, halin da ake ciki yanzu, na alamta barazanar barkewar wani sabon yaki ne a kasar. Nicole Schuweiri, wata kakakin kungiyar fafutukar kare hakkin dan Adam nan, Amnesty International, ta bayyana halin da ake ciki a Iraqin ne da cewar:-

"Abin ban takaici ne, yadda al’amura ke wakana yanzu a Iraqin. Sojojin mamayen ne dai suka janyo hakan, saboda, yayin da suka afka wa Iraqin da yaki, ba su yi tunanin daukan matakan magance matsalolin da za su biyo a baya ba. Amma, abin da ke aukuwa yanzu a nan, wata annoba ce ga rayuwwar dan Adam."

Abin da masharhanta da yawa ke tambaya shi ne: wai shin wannan ba wani bore ne da `yan kasar Iraqin suka tayar, don nuna bacin ransu kamar boren Intifadan da Falasdinawa ke yi ba k Babu shakka, idan aka yi la’akari da yadda matasa ke ta hayaniyar nuna gamsuwarsu da Amirkawan da aka kashe, ake kuma ta nuna gawawwakinsu a bainar jama’a a garin Falluja, idan kuma aka yi la’akari da dauki ba dadin da sojojin mamaye ke ta yi da `yan kasar Irakin a kusan duk fadin kasar, to za a lura a zahiri cewa, ba wasu tsirarun magoya bayan kungiyar Al-Qaeda da na jam’iyar Ba’ath ta tsohon shugaba Saddam Hussein ne ke ta’addanci, kamar yadda Amirka ke kokarin bayyana wa duniya ba. Kamar yadda Abdel Hussein Sha’aban, shugaban kungiyar Larabawa ta kare hakkin dan Adam ya bayyanar:-

"Ai ba za a iya kwatanta wannan arangamar tamkar aikin wasu tsirarun `yan tsageru ba. Ba dai yadda ake ta samun yaduwar rikicin nan a kusan duk fadin kasar ba."

A ganin Abdel Hussein Sha’aban dai, halin da ake ciki yanzu a Iraqin, ya fi yadda Amirka ke yunkurin bayyana wa duniya muni. Yana kuma mai ra’ayin cewa, wannan boren, wata adawa ce ta daddage wa dakarun mamaye, da duk `yan kasar ke yi:-

"Abin da ke faruwa yanzu a Iraqi dai, daddagewa ce, da fararen hular kasar, tare da `yan ta kife masu dauke da makamai, ke yi wa dakarun mamaye a kasar."

A halin yanzu, ba a san yawan magoya bayan shugaban shi’itin nan Moqtada as-Sadr, da ke dauke da makamai ba. Wasu sun ce yana da sojojin kundumbala dubu, wasu sun ce dubu 6, kai wasu ma sun kiyasci ceaw, yawansu ya kai dubu 10. Moqtada Sadr, a yanzu, shi ne ya zamo babban abokin gaban Amirkan a Iraqin. Masu lura da al’amuran yau da kullum dai sun ce, yawan magoya bayansa ya kai dubu dari. Wasu kuma sun ce kusan `yan darikar shi’itin kasar miliyan 5 ne ke goyon bayan ra’ayin da ya bayyana, na mai da Iraqin Jumhuriyar Islama, kwatankwacin Iran.

Kusan kashi 17 cikin dari na al’umman Iraqin ne suka amince da hare-haren da ake ta kai wa dakarun mamaye a kasar, inji sakamakon wani binciken jin ra’ayin jama’ar da aka gudanar. Har ila yau dai, kusan kashi 40 cikin dari ne kuma ke ganin cewa, yakan Iraqi da aka yi, wani wulakanci ne gare su.

A halin yanzu dai, habakar tashe-tashen hankulla, ita ce ke alamta halin da ake ciki yanzu a Iraqin. Kamar dai Nicole Shuweiri da Abdel Hussein Sha’aban, ministan kula da kare hakkin bil’Adama na Iraqin, Abdel Baset Turki, shi ma na ganin cewa, dakarun mamayen ne suka janyo tashe-tashen hankullan da ake yi yanzu a kasar. Ya dai bayyana ra’ayinsa ne kamar haka:-

"A nawa ganin, dakarun mamayen ne suka janyo habakar tashe-tashen hankullan. Da a mai da hankali ne kan tuntubar juna, da kuma z dogara kan masu shiga tsakani, wadanda bangarorin biyu za su fi amincewa da su, da lamarin bai kai ga haka ba."

Daukin da dakarun Amirka suka fara a garin Falluja, da kame wani dan hannun daman Moqtada as-Sadr da suka yi, da kuma umarnin da suka bayar na rufe gidan buga jaridar as-Sadr din, duk wadannan su ne su ka janyo tabarbarewar al’amura a Iraqin.

 • Kwanan wata 08.04.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvkq
 • Kwanan wata 08.04.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvkq