Adama Barrow zai koma Gambiya | Labarai | DW | 25.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Adama Barrow zai koma Gambiya

Adama Barrow zai koma Gambiya ne bayan da Yahya Jammeh ya fice daga Gambiya zuwa Equatorial Guinea.

Wata majiya daga fadar shugaban kasar Senegal ta sanar da cewar zababben shugaban kasar Gambiya Adama Barrow zai koma birnin Banjul a gobe Alhamis da yamma.Adama Borrow wanda ya tsere zuwa Senegal tun a tsakiyyar watan Janairu inda ya sha rantsuwar kama aiki, na shirin komawa gida ne kwanaki kadan bayan da Yayha Jammey ya ficce daga Gambiyar zuwa Equatorial Guinea inda ya samu mafakar siyasa, sakamakon  matsin lambar da ya fuskanta daga Kungiyar kasashen yankin yammacin a Afirka watau ECOWAS.