1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adadin masu neman mafaka zuwa Turai ya ragu

Abdourahamane Hassane
March 20, 2018

Hukumar kididga ta nahiyar Turai Eurostat ta ce kasashen kungiyar tarrayar Turai a shekara da ta shige ta 2017 sun yi rajistar masu neman mafaka dubu 650 abin da hukumar ta ce ke zaman rabi na adadin shekara ta 2016.

https://p.dw.com/p/2uf5V
Libanon Flüchtlingslager Medyen in Bar Elias | Familie Ahmad, Mutter Amina Melhem
Hoto: DW/D. Hodali

'Yan kasasahen Siriya da Iraki da Afghanistan sune suka fi neman mafaka a nahiyar ta Turai a shekar ta 2017 a cewar hukumar ta Eurostat. Kuma daga cikin kasashen da suke kan gaba wajen karbar 'yan gudun hijira sune Jamus da Italiya da Faransa da Girka da Birtaniya da kuma Spain.