Abin fashewa ya raunata mutum 22 a Landan
September 15, 2017Talla
Rundunar 'yan sanda a Britaniyan ta ayyana harin a matsayin na ta'addanci inda ta shawarci al'umma da su guji zuwa wurin da aka samu fashewar da ta haifar da rudani a tashar jirgin a yayin bincike gano wadanda suka kai wannan harin.
Magajin garin birnin Landan Sadiq Khan a jawabinsa ga manema labarai bayan aukuwar lamarin ya yi alla-wadai da abinda ya kira ayyukan muggan mutane da ke anfani da ta'addanci domin hana al'umma walwala, karo na biyar kenan da ake kai wa Britaniya hari a cikin wannan shekara ta 2017.