1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abdullah Gül ya sake baiyana aniyarsa ta neman kujerar shugaban ƙasar Turkiya

August 14, 2007
https://p.dw.com/p/BuE8

Ministan harkokin wajen Turkiya Abdullah Gül ya fara ganawa da shugabannin ´yan adawa a wani yunkuri na samun goyon baya ga hankoronsa na zama sabon shugaban kasar. A karo na biyu jam´iyar AK dake mulki a kasar ta sake nada Gül a matsayin mutumin da zai dare kan kujerar shugaban kasa. To sai dai shugaban jam´iyar adawa mafi girma a Turkiya CHP wati Deniz Byakal ya ce har yanzu ba zai marawa Gül baya ba. Ya ce yana shakka ko Gül zai girmama tsarin mulkin kasar wanda ba ruwansa da addini. Nadin sa da aka yi a cikin watan afrilu ya ci karo da adawa a manyan biranen kasar ta Turkiya abin da ya janyo FM Recep Tayyip Erdogan kiran zabe na gaba da wa´adi.