Abdoullahi Wade ya kai ziyara a yankin Darfur na ƙasar Sudan | Labarai | DW | 07.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Abdoullahi Wade ya kai ziyara a yankin Darfur na ƙasar Sudan

Shugaba Senegal Abdullahi Wade, ya kai ziyara yankin Darfur na ƙasar Sudan.

Wannan ziyara na daga yunƙurin ƙungiyar taraya Afrika, na warware rikicin tawaye a wannan yanki, da ya hadasa mutuwar dubunan jama´a.

Abdoullahi Wade, yayi anfani da wannan dama, inda ya yi kira ga yan tawayen Darfur, baki ɗaya, su mutunta yarjejeniyar zaman lahia, da aka rataba hannu kanta, a birnin Abuja na taraya Nigeria.

Wannan kira mussaman, ya shafi wasu ƙungiyoyin tawaye guda 2, da su ka ƙauracewa yajjejeniyar.

Shugaban ya tantana da Minni Arcua Minnawi, shugaban ƙungiyar tawayen da ta mince da tsagaita wuta, wanda shima ya yi barazanar komawa fagen daga, muddun gwamnatin Khartum, ba ta cika alkawuran da ta ɗauka ba, na naɗa shi, mataimakin mussaman na shugaban ƙasa.

A ɗaya wajen, shugaban ƙasar Senegal, ya gana da Omar El Beshir, inda su ka yi masanyar ra´ayoyi a kann batun aika rundunar shiga tsakani, ta Majalisar Dinkin Dunia a yanki Darfur.

Kazalika,Wade ya tantana da shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas,wanda shima,ya kai ziyara a birnin Khartum.