1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abdallah Gul ɗan takara a zaɓen shugaban ƙasar Turquia

April 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuMx

Bayan dogon lokaci ana kai ruwa rana,tare da dogon turanci, a ƙarshe Jam´iyar AKP mai riƙe da ragamar mulki, a ƙasar Turquia, ta tsaida Abdallah Gul, a matsayin ɗan takara ta a zaɓen shugaban ƙasa.

Abdallah Gul, da ke riƙe da muƙamin ministan harakokin wajenTurquia, ya samu goyan baya, daga mafi yawan yayan jam´iyar.

Babban abokin hamayar sa,wato Praministan Tayyib Erdowan, ya janye takara sa, dalili da rashin samun haɗin kai, daga rundunar soja ta ƙasa.

Ranar juma´a mai zuwa, a ke sa ran majalisar dokoki zata fara kaɗa ƙuri´ar zaɓen shugaban ƙasar.

A taron manema labarai, da ya kira, Abdallah Gul, ya alƙawarta gudanar da aiki, daidai da yadda kundin tsarin mulki ya tanada, tare da kare haƙƙoƙin jama´a.

A nata ɓangare, jam´iyar adawa ta CHP, ta bayyana ƙauracewa zaɓen,a dalili da abun da ta kira, rashin cikkakar demokraɗiya wajen tsaida yan takara.