Abbaliyar ruwa a Faransa | Labarai | DW | 16.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Abbaliyar ruwa a Faransa

Ruwan sama ya yi ta'adi mai yawa a kasar Faransa, inda aka rasa rayuka da dukiyoyi

default

Abbaliyar ruwa

A ƙasar Faransa abbaliyar ruwa da aka yi a kudancin ƙasar, ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 19 yayinda wassu mutane 12 suka ɓace. Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka tabka a yankin ne ya haddasa abbaliyar, inda koguna suka cika suka batse. Jam'ian ceto suna can suna kai dauki, domin kuɓutar da ɗaruruwan mutannen da suka maƙale, kodai cikin motocinsu, ko a gidaje, dama waɗan da suka hau kan rufin kwano don tsira. Dubban gidaje sun kasance babu wutar lantarki an kuma rufe makarantu a ɗaukacin yankin da abinya shafa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal