A Zamanin Baya – Tarihin Afirka
January 18, 2010Talla
A wata fuskar dukkan mutane 'yan Afirka ne. A wannan nahiya ce 'yan Adam suka fara rayuwa. Ƙarnuka da dama bayan haka aka samu manyan dauloli a sassa daban-daban na nahiyar. Amma kuma, daidai da sauran nahiyoyi, ita ma Afirka tana da tabo a tarihinta. Misali dai cinikin bayi ko kuma mulkin mallaka na Turawa.
Sai a biyo mu wajen waiwayar tarihin Afirka da kuma darussan da za a iya koya domin kyautata makomar nahiyar. Domin kuwa Hausawa su kan ce: „Waiwaye, adon tafiya“.
Ba dai wasu litattafai na tarihi ne zamu karanto ba! Shirin na mu zai duƙufa ne kan wata matashiya da ake kira Julie mai son neman sani. Tare da taimakon kakanta ta shiga binciken tarihin nahiyar tasu.