A yau za´a yi taron ƙoli tsakanin Rice da Olmert da kuma Abbas | Labarai | DW | 19.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau za´a yi taron ƙoli tsakanin Rice da Olmert da kuma Abbas

Jim kadan gabanin taron kolin kan yankin GTT, sakatariyar harkokin wajen Amirka C-Rice ta yi kashedi game da sanya dogon buri. Bayan tattaunawar farko da ta yi da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da FM Isra´ila Ehud Olmert Rice ta nunar a Birnin Kudus cewa tun kimanin shekaru 6 da suka wuce sassan biyu ba su gana kai tsaye da juna ba. Ta kara da cewa za´a fuskanci koma-baya saboda har yanzu ba´a kafa gwamnatin hadin kan Falasdinawa tsakanin Hamas da Fatah ba. A jiya lahadi Olmert ya kara jaddada cewar za´a amince da gwamnatin Falasdinawa ne idan Hamas ta yi shailar amincewa da wanzuwar Isra´ila a hukumance. A yau litinin ake ganawa tsakanin Rice da Olmert da kuma Abbas a Birnin Kudus, inda za´a tattauna game da yiwuwar komawa ga shawarwarin samar da zaman lafiya tsakanin Isra´ila da Falasdinu.