A yau za´a yanke shawara wajen ta da Sharon | Labarai | DW | 08.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau za´a yanke shawara wajen ta da Sharon

A wani lokaci yau lahadi likitoci da ke yiwa FM Isra´ila Ariel Sharon magani zasu yanke shawara akan lokacin da zasu ta da shi daga sumar da suka sa shi don kimanta irin barnar da zubar jini da yayi fama da ita, ta yiwa kwakwalwarsa. Likitoci a asibitin Hadassah dake Birnin Kudus sun ce da akwai kyakkyawar alamar cewa FM zai yi rai, amma ba su san iya tasirin da rashin lafiyar zai shafe shi ba. Da farko jami´an asibitin sun ce hoton kwakwalwarsa da aka dauka baya bayan nan ya tabbatar da samun wani dan ci-gaba a mummunan halin da FM mai shekaru 77 da haihuwa ke ciki. An yiwa Sharon dai tiyatar gaggawa har sau uku a kokarin tsayar da zubar jini a kwakwalwarsa tun bayan ya fuskanci mummunar mutuwar jiki a ranar laraba da ta wuce.