A yau za´a gana tsakanin Bush da shugaba Hamid Karzai a Camp David | Labarai | DW | 05.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau za´a gana tsakanin Bush da shugaba Hamid Karzai a Camp David

Har yanzu ´yan kasar KTK 21 da ake garkuwa da su a Afghanistan na cikin mawuyacin hali. Kungiyar Taliban ta sake hana likitoci su duba marasa lafiya daga cikin su mutanen da ta ke garkuwa da su. Kakakin Taliban Qari Yussif Ahmadi ya ce ba su amince da likitocin ba. A daura da haka ya nuna shirin ganawa ido da ido da masu shiga tsakani na KTK ko da wani wuri ne da ba ya karkashin ikon ´yan Taliban. To amma ya ce dole sai MDD ta ba da tabbacin tsaron lafiyar ´yan Taliban tukuna. Har yanzu ma dai ba´a san makomar Bajamushen nan da shi ma ake garkuwa da shi a Afghanistan ba. Garkuwar da ake yi da ´yan kasashen ketare a Afghanistan zata zama wani batun da za´a tattauna kai tsakanin shugaban Amirka GWB da takwaransa na Afghanistan Hamid Karzai a wata ganawa da zasu yi yau a wurin shakatawar shugaba Bush dake Camp David.