1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yau za´a ba da sakamakon hukuma na zaben Iraki

January 20, 2006
https://p.dw.com/p/BvBT

Masu sa ido a zabe na kasa da kasa na da ra´ayin cewa a wurare da dama an kamanta gaskiya a zaben ´yan majalisar dokokin Iraqi da aka gudanar a cikin watan desamba. A cikin sanarwar karshe da suka bayar akan zaben, masu sa idon sun ce duk da haka an tabka ba daidai ba amma hakan bai taka kara ya karya ba. A wani lokaci yau din nan ne a hukumance za´a ba da sakamakon karshe na wannan zabe, wanda ´yan sunni suka yi zargin tabka magudi a ciki.