A yau za a yi jana´izar Bhutto a mahaifarta dake kudancin ƙasar | Labarai | DW | 28.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau za a yi jana´izar Bhutto a mahaifarta dake kudancin ƙasar

Ana samun munanan tashe-tashen hankula a faɗin kasar Pakistan bayan kisan gillan da aka yiwa tsohuwar Firaministan ƙasar kuma shugabar ´yan adawa Benazir Bhutto. Rahotanni sun yi nuni da cewa an halaka mutane da yawa. Tashe-tashen hankulan sun fi yin muni ne a lardin Sindh inda Bhutto ɗin ta fito sai kuma a birnin Karachi. An yi ta cunnawa motoci da gine-ginen gwamnati wuta yayin da wasu kuma suka yi ta kwasan ganima a kantuna kana kuma aka yi ta toshe hanyoyi da tayoyin mota. A halin da ake ciki an kai gawarta a kudancin ƙasar inda za´a yi mata jana´iza in an jima. Shugaba Pervez Musharraf yayi kira ga al´umar ƙasar da su kwantar da hankulansu sannan ya ba da umarnin zaman makoki na kwanaki uku. Kantuna da makarantu zasu kasance a rufe a tsawon waɗannan kwanaki uku. Tsohon firaminista Nawaz Shariff ya ce zai ƙauracewa zaben ´yan majalisar dokoki da aka shirya gudanarwa a ranar takwas ga watan janeru mai zuwa, sannan yayi kira ga shugaba Musharraf da yayi murabus don ceto ƙasar. Kafofin yaɗa labaru da dama sun rawaito ƙungiyar al-Qaida na cewa ita ke da alhakin kai harin da yayi sanadiyar mutuwar Bhutto.