a yau waadin da Kungiyar turai ta bayar na cafke Mladic yake cika | Labarai | DW | 30.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

a yau waadin da Kungiyar turai ta bayar na cafke Mladic yake cika

A yau waadin da Kungiyar Taraiyar Turai ta bayar na cafke Ratko Mladic da ake nema ruwa a jallo saboda laifukan yaki daya tabka a lokacin yakin Bosnia,yake cika ba tare an gano inda yake ba.

Kungiyar, tace zata dakatar da tattaunawa akan batun shigar Serbia-Montenegro,cikin kungiyar,muddin dai bata mika Mladic ga kotun kasa da kasa dake Hague ba zuwa ranar 30 ga wannan wata na Afrilu ba.

A ranar jumaa ne dai komishina mai kula da fadada kungiyar Olli Rehn ya sake tabbatar da wannan barazana.

Serbia a nata bangare tace har yanzu tana neman Mladic,wanda ake tuhuma da laifin kisan kiyashi tun 1995.