A yau ne kwamitin lambar yabo ta Nobel ya fara ba da sanar da sunayen wadanda suka cancanci samun lambar yabo a wannan shekarar | Siyasa | DW | 04.10.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

A yau ne kwamitin lambar yabo ta Nobel ya fara ba da sanar da sunayen wadanda suka cancanci samun lambar yabo a wannan shekarar

A fannin binciken kimiyyar kiwon lafiya bana za a mika lambar ne ga Richard Axel da Linda B- Buck dukkansu 'yan kasar Amurka sakamakon nasarar bincikensu akan abubuwan dake taimaka wa dan-Adam wajen sunsuno da banbanta kamshi da karni

Kamuwa da mura ta wadatar wajen fahimtar muhimmancin ikon sunsuno ga rayuwar dan-Adam ganin yadda hancinsa kan toshe kwata-kwata. Domin kuwa idan mutum ba ya jin kamshin abu sai ka ga baya kwadayin kome. Kuma ko da yake, bisa sabanin dabbobi, rayuwar dan-Adam ba ta ta’allaka kwata-kwata da ikonsa na sunsunan abu ba, amma fa abu ne dake da muhimmanci ga jin dadin rayuwarsa. Allah Yayi wa dan-Adam baiwar banbanta kamshi ko wari ko kuma karnin abubuwa kusan dubu 10. Richrd Axel da Linda B. Buck sun gudanar da bincike akan yadda lamarin ke gudana. A lokacin da yake bayani a game da rawar da gaggan masana kimiyyar guda biyu suka taka, Göran Hansson, shugaban kwamitin lambar yabo ta Nobel cewa yayi:

A sakamakon binciken nasu a yanzu mun kara fahimtar yadda jikin dan-Adam ke aiki. Kuma nan ba da dadewa ba za a shiga amfani da sakamakon binciken nasu a matakan kiwon lafiya.

Lambar ta yabo an gabatar da ita ne ga Axel da Buck dagane da binciken yanayin aikin jinkin dan-Adam amma ba yadda kiwon lafiyarsa ke gudana ba, bisa sabanin yadda aka saba gani a sauran kyaututukan yabo daga kwamitin na Nobel. Yau dai sama da shekaru dari ke nan da aka ankara da cewar can a kuryar hancin dan-Adam akwai wani abin dake taimaka masa wajen sunsuno da rarraba kamshi da karnin abubuwan da yake shaka, amma kawo yanzun ba wanda ya san yadda lamarin ke tafiya, sai bayan binciken da masana kimiyyar guda biyu suka gudanar. A shekarar 1991 ne masana kimiyyar su biyu suka gabatar da wani nazari na hadin guiwa dangane da abubuwan dake ba wa dan-Adam ikon sunsuno daga kuryar hancinsa. Bayan haka suka ci gaba da ayyukansu na bincike a wawware. Dukkansu biyu sun gano wani dangi na halitta dake taimakawa wajen daidaita shakar kamshi ko karni a hancin dan-Adam. Bisa al’ada dai kwamitin lambar yabo ta Nobel din ne ke gabatar da sunan wadanda suka cancanci samun lambar a bainar jama’a, amma Richard Axel ya samu wannan labarin ne kai tsaye daga gidan rediyon kasar Sweden. A dai ranar 10 ga watan desamba ne za a mika wa masana kimiyyar guda biyu kyautar wacce ta kunshi Euro miliyan daya da dubu dari a can Stolkholm ta kasar Sweden.