A yau ministocin manyan kasashen duniya suke ganawa game da shirin nukiliya na Iran | Labarai | DW | 08.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau ministocin manyan kasashen duniya suke ganawa game da shirin nukiliya na Iran

A yau ministocin harkokin wajen manyan kasashen duniya guda 6 suke ganawa a birnin New York,a kokarinsu na samo hanya sahihiya wadda zaa tilastawa Iran dakatar da aiyukanta na nukiliya da suke ganin na kera makaman kare dangi ne.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka,Condoleeza rice zata karbi bakuncin takwarorinta daga Burtaniya,Sin,Faransa,Jamus da Rasha da kuma kungiyar taraiyar turai,wajen wata liyafa da zasu tattauna watsi da bukatun majalisar dinkin duniya da Iran take ci gaba dayi.

Shugaba Jacques Chirac na Faransa da shugabar gwamnatin Jamus angela Merkel, a jiya lahadi suka fito da wata takarda ta hadin gwiwa,inda sukayi kira ga majalisar data dauki tsatsauran mataki da zai tilastawa Iran dakatar da shirinta na inganta sinadarin uranium.